• Sun. Sep 8th, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Yadda Aka Fasa Wani Aure A Jihar Sokoto Bayan Iyayen Amarya Sun Gano Ango Ya Fadi Jarabawar Kammala Jami’a

ByLucky Murakami

Sep 9, 2022

An fasa wani aure a jihar Sokoto bayan iyayen yarinya sun gano cewa angon ‘yar su ya taba samun Spill Over a Jami’a.

Iyayen yarinyar sun ce sun dauki wannan mataki ne domin suna tsoron kar a haifar misu jikoki dakikai ne.

Iyayen yarinya sun ce sun gano wannan ne ana saura sati daya auren sa da ‘yar su.

Wannan lamari dai ya faru ne a jihar Sokoto kamar yadda majiyarmu ta tabbatar.

Mata Ta Yi Garkuwa Da Mijinta Kan Rashin Kwanciyar Aure

Wata matar aure da ta yi garkuwa da mijinta ta karbi kudin fansa ta shiga hannun hukuma.

Dubun matar ta cika ne bayan sun karbi kudin fansa Naira miliyan biyu bayan ta yi garkuwa da mijin nata.

Sai dai ta shaida wa ’yan sanda cewa, “Wanda ya yi garkuwa da shi ya karbi kudin fansa Naira miliyan biyu, amma bai ba ni kasona daga ciki ba, ko kamannin kudin ban gani ba.”

Ta bayyana cewa ta sa an yi garkuwa da shi ne saboda rashin kwanciyar aure da ita da kuma watsi da ’ya’yansu.

Matar dai tana cikin mutum 29 da ’yan sanda suka gabatar wa ’yan jarida kan zargin garkuwa da mutane da sauran laifuka aa Jihar Akwa Ibom.

A cewarta, sakamakon watsi da ita da maigidanta ya yi ta fara yin aikatau domin ciyar da kanta da ’ya’yansu bayan mijin ya auri wata mata.

Hakan ne, a cewarta ya tilasta ta kitsa sace shi domin ta samu kudin kula da kanta da ’ya’yanta daga hannunsa, amma ta yi rashin sa’a asirinsu ya tonu ba tare da an ba ta rabonta daga cikin kudin ba.

Magidancin da aka kubutar, ya ce tun ranar 21 ga watan Yuli, 2022 aka yi garkuwa da shi a harabar gidansa.

Da yake jawabi, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Akwa Ibom, Olatoye Durosinmi, ya ce rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba, wajen murkushe ayyukan laifi a fadin jihar.

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

One thought on “Yadda Aka Fasa Wani Aure A Jihar Sokoto Bayan Iyayen Amarya Sun Gano Ango Ya Fadi Jarabawar Kammala Jami’a”
  1. Wannan labarin naku Qaryace tsagaronta ku ke ma jahar Sokoto, azahirin gaskiya yakamata Wakilin wannnan gidan jaridar yanuna kwarewar shi a wurin aiki na gidan jarida.

    A lokacin da yaje dauko wannan rahoto indai akwai kwarewa a wurin aikin gidan jarida yakamata yasanar da masu karantawa abun ya faru ne acikin Local government area ka za da ka za acikin unguwar….

    Amma babbar matsalar itace ba’a samu wannan rahoton hakan ba, wanda yin hakan ya nuna cewa wannan Qagin labari ne akawa Sakkwatawa.

    Agurguje yanada kyau ku Qara sa hikima da tunani mai kyau kafin a wallafa labari ko yaya abun yake.

    Sidi Umar
    Sokoto State.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *