Close Menu
    AMIHAD.COM
    • Admission
    • Education
    • Finance
    • Scholarship
    • Tech
    • Visa
    AMIHAD.COM
    News

    Yadda Aka Kama Dan Sanda Yana Lalata Da ‘Yar Dan Uwansa

    Lucky MurakamiBy Lucky MurakamiJuly 29, 2022No Comments2 Mins Read

    Labarin da muke samu shine an tsare wani Sufeto kuma jami’i tawagar sirri ta musamman a Rundunar ’Yan Sandan Jihar Nassarawa, bi sa zargin yi wa ’yar dan uwansa da yake riko fyade.

    Shugaban Kungiyar Lauyoyi Mata ta Kasa Rabi’atu Addra ce ta bayyana hakan ga manema labarai a Lafiya da ke jihar ranar Laraba.

    Ta ce wani ne ya kai wa kungiyar rahoton lamarin, kuma ba su yi kasa a guiwa ba suka shiga bincike.

    Ta bayyana cewa an kama dan sandan tare da jaddada tsayuwar dakarsu don ganin an yanke masa hukunci daidai da abin da ya aikata, don hakan ya zamo izina ga na gaba.

    Ta kuma yi kira ga ’yan Sanda da su tabbatar da bincike mai zurfi kan lamarin, domin adalci ga wacce aka zalunta.

    [ads1]

    “Muna samun labari muka hada kai da Kungiyar Yaki da Cin Zarafin Mata da Kananan Yara da kuma rundunar ’yan sanda domin damko wanda ake zargin,” in ji ta.

    “Ita kuma yarinyar mun kai ta asibiti mun biya mata kudin magani, sai dai dan nata mai watanni shida a duniya ya rasu.

    “Ma’aikatar Shari’a ta jiha ma ta biya kudin gwajin kwayar halitta domin ci gaba da tattara hujjoji kan lamarin.”

    Hajiya Rabi’atu ta ce tuni sun sada yarinyar da ahalinta, wacce mutuwar mahifinta ce tun farko ta sanya ta komawa hannun wanda ake zargin.

    Har zuwa lokacin hada wannan rahoto kakakin ’yan sandan Jihar Nasarawa DSP Ramhan Nansel bai ce komai ba kan lamarin, kuma ya ki amsa kira da sakon waya.

    Allah yasa mu dace ameen

    Related Posts

    Tofah Bayan Ganin Bidiyon Tinubu Yana Motsa Jiki, Malmai Sun Fara Zazzago Martani

    January 11, 2024

    Yadda Wata Matar Aure Ta Kama Mijinta Yana Cin Amanarta Ba Kunya Ba Tsoron Allah

    December 25, 2022

    Karshen Duniya Yazo: Yadda Dalibi Ya Dirkawa Malamarsa Ciki

    December 12, 2022

    Wani Dalibi Ya Kashe Kansa Saboda Ya Kasa Mallakar Wayar Naira Dubu Hamsin

    November 27, 2022

    An Kama Likitan Bogi Daya Dirkawa Yan Mata Hudu Ciki

    November 26, 2022

    Yadda Mahaifiyar Budurwa Tasa Saurayi Ya Dirkawa ‘Yarta Ciki

    November 25, 2022
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    • About Us
    • Contact Us
    • Disclaimer
    • Privacy Policy
    • Terms & Conditions
    Copyright © 2025 AMIHAD.COM | All Right Reserved.

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.