• Sat. Jun 22nd, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Yadda Aka Kama Kwarto Yana Lalata Da Matar Aure A Bandaki

ByLucky Murakami

Nov 7, 2022

Wani labari daga garin Owerri na jihar Imo ya nuna cewa dubun wani matashi mai suna Dona ya cika bayan an kama shi turmi tabarya yana zina da wata matar aure mai suna Julie a cikin wani daji a gefen garin Umuoba Uratta a karamar hukumar Owerri ta arewa ranar Juma’a.

Bayanai sun nuna cewa Julie uwa ce ga yara biyu wacce ake zargin cewa tana bin maza.

Wasu matasa ne suka sa ido bayan an bukaci su yi haka a kan harkokin Julie, kuma suka yi sa’a bayan ranar Juma’a Juli ta shiga daji bayan ‘yan mintoci sai Dona ya bi ta zuwa cikin dajin.

The Punch ta ruwaito cewa ganin haka ya sa matasan suka bi masoyan zuwa cikin daji inda suka kama su turmi tabarya suna lalata. Nan take wani matashi ya dauke wando da pant na Dona wanda ya tube ya dora akan wayar salularsa.

Daga bisani bayanai sun nuna cewa Julie ta bukaci matasan su rufa mata asiri ita kuma za ta basu N5.000 domin su saye kwalaben barasa amma matasan suka ki.

Kakakin hukumar yansanda na jihar Imo ya shaida wa wani dan jarida cewa labarin lamarin bai iso ofishinsa ba a lokacin da aka tambaye shi.

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *