Wani fasto ya yi wa wasu kananan yara ’yan uwan juna fyade har daya daga cikinsu ta samu juna biyu.
Yarinyar da wannan fasto ya dirka wa ciki tare da ’yar uwarta mabiyansa ne a wani cocin Cherubim And Ceraphim da ke Jihar Ogun.
Kakakin ’yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, ya ce, “kananan yaran sun bayyana cewa idan suka je addu’ar dare a cocin, faston kan kai su gidansa, ya tursasa su tsoti wani wanda ke sa su barci nan take, idan sun farka za su ga an yi amfani da su.
“Da aka tambaye su abin da ya hana su fada wa kowa, sun ce faston ya yi barazanar kashe su idan suka kuskura suka gaya wa wani.”
Oyeyemi, ya ce faston, mai shekara 30, ya shiga hannun, bayan mahaifin yaran ya kai kara Ofishin ’yan sanda.
Ya ce mahaifin kananan yaran ya kai kara ne bayan ya gano cewa babbar mai shekara 16 tana dauke da juna biyu.
Ya bayyana cewa limamin cocin ya amsa zargin da ake masa a lokacin da ’yan sanda ke masa tambayoyi.
Ya kara da cewa Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Ogun, Lanre Bankole, ya sa a gudanar da cikakken bincike kan lamarin sannan a gurfanar da malamin addinin a kotu.