Bayan kama matar aure dumu-dumu da gardi, an tilasta mata zagaya kauye da mijinta a kafadarta.
A wani labarin, an tirsasa wata matar aure ta dauka mijinta a kafadunta kuma ta zagaye titunan kauyensu bayan an kama ta dumu-dumu da wani gardi.
Shafin LIB ya ruwaito cewa, lamarin ya faru ne a kauyen Borpadaw aake Indiya a ranar 3 ga watan Yulin 2022.
Matar tayi batan-dabo na tsawon sati kuma mijinta da sirikanta sun dinga nemanta amma basu ganta ba.
A gefe guda kuma Wata mata mai suna Aba ta bada labarin yadda tayi ciki tare da haifo zukeken yaro namiji ba tare da ta kwanta da namiji ba.
A yayin tattaunawa da mai siyar da ruwa a bakin titi, ta bayyana cewa shekarunta 4 rabon da ta kwanta da namiji.
Kwatsam cikinta ya fara kumbura tare da ciwo, koda taje asibiti sai aka ce aiki za a yi mata a ciro ciwon dake cikinta.
Tace kawai ta ji tana son ciro abinda ke cikinta ba tare anyi mata aiki ba, lamarin da yasa tayi nishi har yaro namiji ya fado.