Rahoton da muka samu shine ’Yan sanda a jihar Anambra sun cafke wani mai suna Chisom Nwekeda ya kware wajen yin amfani da asiri don damfarar masu sana’ar POS a Awka, babban birnin jihar da kewaye.
Jaridar Aminiya ta rawaito cewa matashin, ma
i kimanin shekara 26 ya shiga hannu ne ranar 15 ga watan Satumban 2022 a karamar hukumar Amawabia da ke jihar.
A cewar wata sanarwa da Kakakin rundunar a jihar, Ik
enga Tochukwu ya fitar ranar Alhamis, tuni wanda ake zargin ya amsa aikata laifin da ake zarginsa da shi kamar yadda majiyar amihad.com ta tabbatar.
Ikenga ya ce binciken farko-farko ya nuna cewa wanda ake zargin yakan yanka fararen takardu ne daidai dz tsayin takardun kudi sannan ya ba masu POS da nufin su saka masa a asusun ajiyarsa na banki.
Kakakin ya kuma ce yanzu haka rundunar na kokarin ganin yadda za ta kamo ragowar abokan damfarar Chisom din nan ba da jimawa ba.