Diniya ina zaki damu, hakika wadannan abubuwa da suke faruwa suna ci gaba da tabbartar mana da cewa duniya tazo karshe.
Labarin da muke samu shine wani matashi mai suna Abubakar Hamidu, ya fada komar ’yan sanda a Jihar Gombe kan zargin yi wa kanwarsa fyade.
Majiyar amihad.com ta tabbartar mana da cewa matashin mai kimanin shekaru 35 da ke zaune a Unguwar Jauro Abare, ana zarginsa da yin lalata da ’yan uwar tasa har sau biyu a lokuta daban-daban.
Da yake gabatar da wanda ake zargin ga manema labarai, Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Gombe, Ishola Babatunde Baba’ita, ya ce wani mai suna Muhammad Hamza ne ya shigar da karar matashin a ranar 19 ga watan Yulin da muke ciki.
Baba’ita ya ce mai shigar da karar wanda ke zaune a Unguwar Kasuwar Mata, ya kai wa ’yan sanda korafin cewa wanda ake zargin ya yi lalata da kanwar tasa ce karon farko a wani gida da ya zama kufai a Unguwar ta Jauro Abare.
Kwamishinan ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yan sandan, ASP Mahid Mu’azu, ya ce an sake kama matashin karo na biyu yana aikata masha’ar da kanwar tasa a bakin wani tafki.
A cewarsa, da zarar sun kammala bincike za su tura wanda ake zargin zuwa kotu domin ya fuskanci shari’a.