AMIHAD.COM
    • Admission
    • Education
    • Finance
    • Scholarship
    • Tech
    • Visa
    AMIHAD.COM
    Home » Yadda Aka Kama Me Wankin Mota Da Yarinya Yar Shekara Sha Daya
    News

    Yadda Aka Kama Me Wankin Mota Da Yarinya Yar Shekara Sha Daya

    Lucky MurakamiBy Lucky MurakamiJuly 17, 2022Updated:August 27, 2022No Comments2 Mins Read
    Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr WhatsApp Email
    Share
    Facebook Twitter LinkedIn WhatsApp Pinterest Email

    Wata yarinya ‘yar shekara 11 ta shaida wa kotun sauraron masu aikata laifukan fyaɗe da cin zarafi ta Ikeja, jihar Legas, yadda wani mai wankin mota Ezekiel Udoh, mai shekara 39, yayi mata fyade sannan ya ɗirka mata ciki. LH na wallafa

    Jaridar The Punch ta samo cewa lamarin ya auku ne a yankin FESTAC Town, na jhar a shekarar 2020.

    Jami’in ɗan sanda mai tuhuma, Z.A Dindi shine ya jagoranci yarinyar wurin bayar da shaidu.

    Yarinyar ta bayyana yadda yayi mata fyiɗe

    Da take labartawa kotu yadda lamarin ya auku, yarinyar tace wanda ake zargin yayi amfani da ita har sau biyu.

    A karon farko da abin ya faru, tace aikenta yayi bayan ta dawo ya sanya ta kai masa saƙon ɗaki, inda yayi mata fyiɗe.

    Ta bayyanawa kotu cewa:

    Udoh ya aikeni na siyo masa wani abu, bayan na dawo, ya ce min na kai masa sama. Bayan na kai sai yace na sanya masa a ɗakin shi inda anan yayi amfani dani a karon farko. Yace idan na faɗawa wani sai ya kashe ni.

    A lokacin da yayi amfani dani a karo na biyu, na ga jini yana fitowa ta gaba na. Bansan cewa ina ɗauke da ciki ba. Kakata ta tambayeni meyasa nake ƙiba na ce ban da masaniya.

    Ta haifi ɗa namiji

    Yarinyar wacce yanzu ta kai shekara 13 a duniya, ta haifi ɗa namiji wanda yanzu haka yake da shekara ɗaya da wata biyar a duniya.

    An ɗage sauraron ƙarar har zuwa 29 ga watan Satumba, 2022.

    Share. Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr WhatsApp Email

    Related Posts

    Yadda Wata Matar Aure Ta Kama Mijinta Yana Cin Amanarta Ba Kunya Ba Tsoron Allah

    December 25, 2022

    Karshen Duniya Yazo: Yadda Dalibi Ya Dirkawa Malamarsa Ciki

    December 12, 2022

    Wani Dalibi Ya Kashe Kansa Saboda Ya Kasa Mallakar Wayar Naira Dubu Hamsin

    November 27, 2022

    An Kama Likitan Bogi Daya Dirkawa Yan Mata Hudu Ciki

    November 26, 2022

    Yadda Mahaifiyar Budurwa Tasa Saurayi Ya Dirkawa ‘Yarta Ciki

    November 25, 2022

    Yadda Aka Kama Malamin Addini Yana Lalata Da Yan Mata Biyu Yan Uwan Juna

    November 23, 2022
    Add A Comment

    Leave A Reply Cancel Reply

    Check Also

    Ya Kamata Kusan Da Wadannan Tsaruka Na Tallafi Da Ake Bawa Yan Nigeria

    January 27, 2023

    FG Begins SMEDAN ₦1.5m Loan – Application Portal

    January 20, 2023

    How to Obtain an Ecowas ePassport as a Holder of a Nigerian Passport

    January 20, 2023

    Easy Way to Apply for a Visa in Nigeria

    January 20, 2023

    Apply 2023 Microfinance Bank Kaduna Recruitment

    January 20, 2023
    • About Us
    • Contact Us
    • Disclaimer
    • Privacy Policy
    • Terms & Conditions
    Copyright © 2023 AMIHAD.COM | All Right Reserved.

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.