Alkalin wani kotu dake Oke-Ogbere a garin Ibadan, na jihar Oyo ya warware auren wata mata mai suna Temilade Oyeyemi da mijin ta Ayo Oyeyemi a ranar Alhamis.
Alkalin kotun mai suna Sulaiman Olaniyi ya warware auren ma’auratan ne a dalilin gamsassun shaidu da aka bayyanar a gabansa wanda suka nuna cewa lallai Ayo makaryaci ne kuma maciyi amanar matarsa ne.
Temilade mai shekaru 28 ta bayyana wa kotu yadda mijinta ya ci amanar ta bayan ya gabatar da budurwarsa a matsayin kanwar mahaifiyarsa wa ita da iyayenta.
” Wannan na daga cikin dalilan da yasa iyaye na suka amince mu yi aure shekara uku da suka wuce.
Temilade ta ce ta fara fahimtar karya da cin amanar da Ayo yayi mata ne wata ranar da da dare bayan auren su inda ta gan shi kuru-kuru yana saduwa da matar da ya gabatar a matsayin kanwar mahaifiyar sa.
” Kafin wannan rana dama kullum idan dare ya yi sai ya tashi daga kan gadon da muke kwance tare ya koma kasa inda wannan mata ke kwance. Idan na yi magana sai yace ai ya kwanta a kasa ne sabo da zafi ya yi yawa.
“Bayan na samu ciki sai ya juya min baya ya fara tozarta ni ya daina kula ni kwata-kwata.
Shi kan sa Mahifin sa da ya bayyana a kotun dakan sa ya roki kotu da ta raba wannan aure, domin cin amanar ta yi yawa.
” Ayo ya bani kunya sannan ya tozartani a idunun duniya ace a a matsayin sa na da na. Dama can ya dai na kulawa da ni, hasali ma kawai ganin sa muka yi wai har yayi aure ya na ma da da.”
Sai dai kuma Ayo ya karyata wannan zargi da ake masa. Ya ce duk zuki ta malle ne ba haka bane.
Yace ” Tun da na auri Temilade ni ne wanki, ni ne shara kuma ni ne nake fita in nemo na kawo mata. Ba irin wannan magana.”
A karshe alkalin kotun Sulaiman Olaniyi ya raba auren, sannan ya ce ita Temi ne zata ci gaba da rike dan nasu.