’Yan sanda a jihar Ogun sun kama wani tsoho mai shekara 84 bisa zargin yi wa ’yar shekara takwas fyade.
An kama tsohon wanda ke zaune a unguwar Okun Owa da ke Ijebu Ode a Jihar Ogun ne bayan wani rahoto da aka kai babban ofishin ’yan sanda da ke sashen Obalende.
Majiyarmu jaridar Aminiya ta rawaito cewa kakakin ’yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, ya shaida wa ’yan jarida a ranar Asabar cewa mahaifin yarinyar ya kai wa ’yan sanda kara ne bayan ya gano ’yarsa na zubar da jini daga al’aurarta.
A cewarsa, mahaifin yarinyar ya ce lokacin da ya tambaye ta dalilin zubar jinin, sai ta sanar da shi cewa wanda ake zargin ne ya yi lalata da ita.
Oyeyemi ya ce nan take DPO na Obalende, Murphy Salami tura jami’an bincikensa zuwa wurin, inda aka cafke “tsohon”.
“Bincike na farko da aka yi ya nuna cewa tsohon ya yi kaurin suna wajen lalata kananan yara a yankin,” in ji shi.
Oyeyemi ya ce an kai yarinyar zuwa Babban Asibitin Ijebu Ode domin kula da lafiyarta.
Ya kara da cewa Kwamishinan ’Yan Sanda, Lanre Bankole, ya bayar da umarnin mika wanda ake zargin zuwa sashen binciken manyan laifuka na jihar domin gudanar da bincike tare da gurfanar da shi gaban kuliya.