An kama wani magidanci a yayin da yake tsaka da lalata da ’yar cikinsa mai shekara 11.
Magidancin mai ’ya’ya uku ya zakke wa karamar yarinyar ce a lokacin da matarsa ke tsaka da bacci bayan da yarinyar ta je karbar wayarsa da nufin za ta yi kallon fim a ciki.
uban yana tsaka da aikata masha’ar tasa ne wani jami’in ‘Civil Defence’ ya ritsa shi.
“Lokacin da yarinyar ta zo tashi na matata na bacci, ban yi mata komai ba, amma dai na dan taba wani sashe na jikinta,” inji magidancin bayan an kama shi.
Hukumar ‘Civil Defence’ ta Jihar Kwara ta ce magidancin ya kunna wa ’yar tasa wani fim a wayarsa, wanda ya yi amfani shi wajen jan hankalinta.
Da yake tabbatar da lamarin, kakakin ‘Civil Defence’, reshen jihar, Babawale Afolabi, ya ce an dauke yarinyar zuwa asibiti don bincikar lafiyarta.
Babawale, ya kara da cewa za a mika wanda ake zargin zuwa kotu da zarar an kammala bincike.