• Sat. Jun 22nd, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Yadda Aka Kama Wani Matashi Yana Lalata Rayuwar Yarinya

ByLucky Murakami

Aug 16, 2022

Innalillahi wa’inna ilaihirraju’un, duniya ina zaki damu ne? Daga wannan sai wannan yanzu rayuwa ta zama abun tsoro ta yadda kullum sai wani sabon aikin ashsha ya bulla.

A wani labari da muka samu ta wanda jaridar Hausaloaded ta rawaito wani Saurayi Mai tashen balaga dubunsa ya cika bayan da wani Dan sa ido ya ganoshi yana lalata da wata karamar yarinya ‘yar furamari.

Jin motsin su ne daga cikin daji bayan makarantarsu, yasa wannan Dan sa idon ya nemi sanin abunda yake motsawa anan.

Sai dai abun mamaki sai ga wannan matashin ya himmatu wajen yin lalata da yarinyar da ake mata ganin karamace.

Sai dai bincike ya tabbatar da cewa matashin ya dade yana jiyar da wannan kwalar dadin Jima’i. Wanda hakan yasa duk lokacinda ya bukaceta da wasu abokanta suke bashi hadin kai.

Yana da kyau iyaye musaka idanuwa sosai aka irin makarantar da muka sa yaran mu da kuma bibiyan abubuwan da ke wakana bayan dawowatsu gida.

Allah Ya shirya mana.

 

Me Yayi Zafi Uwa Tayi Shelan Neman Wanda Zai Kashe Mata Dan Ta Da Ta Haifa Na Cikinta

Wata mahaifiya a garin Zariya Jihar Kaduna, ta Shaidawa Jami’an tsaro na ‘Yan Sanda Shiyyan Zariya cewa, da Allah Zai kawo Wani mutum dan albarka da zai Zama Silar mutuwar Dan cikinta da Sai ta kwana tana Masa addu’ar Allah ya biya shi, ita a nufinta akashe kawai kota halin Kaka Saboda yafi karfinta, kullum shikenan hadata rigima da al’umman gari.

Usman Shine Sunan Matashin, Wanda mahaifiyarsa ta gaji da ganinsa a doron Kasa, Saboda irin rigimar da yake dauko Mata, yau Shine ya Sari wancan gobe ya Soke wancan.

Hakan ya Kara bude Wani Sabon fai-faine, a dalilin yadda Matashin ya Sossoki Wani Dan uwansa Matashin Mai kimanin Shekara 29 da wuka, har sai da lamarin ya Kai ga Yan Sanda, “Inda aka bukaci mahaifiyar Wanda ya aikata wannan mummunar ta’asar data bayyana a gaban hukuma duba ga yadda Shi Dan nata yayi na Kare.

Wakilin amihad.com ya bibiyar lamarin ya Kuma tabbatar da wannan kalamin da mahaifiyar Usman din tayi gaban ‘Yan Sanda, Mahaifiyar ta Cigaba da Shaidawa Jami’an tsaro ita Bata San inda Dan nata ya shiga ba amsar da ta baiwa Jamian tsaron kenan bayan tambayarta da Jami’an tsaron Suka Yi, Shin ko ta San inda dan nata ya Shiga?

Bisani yadda Jami’an tsaron ke sintirin farautar Usman din a domin ya gurfana gaban hukuma Kan irin ta’asar da yayi, Amma an nemi Shi matashin Sama ko Kasa Babu labarinsa, a takaice dai Saboda irin gundurar da mahaifiyar tayi da Dan nata har ya kai ga ta Shaidawa Jami’an tsaro cewa, ita kawai mummunar ajalin Dan nata take jira Allah ya nuna Mata tun tana Raye.

Shidai Matashi Usman Haifaffen Tudun wadan Zariya ne, dan Wani Shiyya da ake Kira da gangaren kwadin Usman ya addabi Al’umma kullum jangwamoma mahaifiyarsa rigima yake yi, bakin ciki yau daban ta gobe daban

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *