AMIHAD.COM
    • Admission
    • Education
    • Finance
    • Scholarship
    • Tech
    • Visa
    AMIHAD.COM
    Home » Yadda Aka Kama Wani Matashi Yayi Wa ‘Yar Makwabcinsa Fyade
    Family & Relationships

    Yadda Aka Kama Wani Matashi Yayi Wa ‘Yar Makwabcinsa Fyade

    Lucky MurakamiBy Lucky MurakamiSeptember 2, 2022Updated:October 6, 2022No Comments3 Mins Read
    Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr WhatsApp Email
    Share
    Facebook Twitter LinkedIn WhatsApp Pinterest Email

    Asirin wani matashi ya tonu inda aka kamashi da lalata rayuwar diyar makwabcinsa kamar yadda majiyarmu ta tabbatar.

    Jaridar Premium Times ta rawaito cewa kotun majistare dake Ogundu jihar Legas ta yanke wa wani matashi mai suna Ifeanyi Onyega mai shekara 22 daurin zaman gidan kaso bayan ta kamashi da laifin yi wa ‘yar makwabcinsa mai shekara 16 fyade.

    Alkalin kotun M.O. Tanimola ta yi watsi da rokon sassauci da Onyega ya yi.

    Tanimola ta ce Onyega zai ci gaba da zama a kurkuku har sai ta kammala yin shawara da DPP.

    Ta ce za a ci gaba da shari’a bayan 21 ga watan Otoba.

    A zaman da kotun ta yi ranar Alhamis lauyan da ya shigar da kara Donjour Perezi ya ce Onyega dake zama a layin Adebimpe dake unguwan Kosofe ya aikata wannan ta’asa ranar 31 ga Yuli a gidansa.

    Perezi ya ce a wannan rana Onyega ya kira ‘yar makwabcinsa cikin dakinsa domin ya aike ta amma sai ya danne ta a dakin.

    Lauyan ya ce Onyega ya ja wa yarinyar kunne da idan ta fadawa wa wani abin da ya faru da ita zai kashe ta.

    “Sai dai yarinyar ta fada wa mahaifiyar ta abin da ya faru inda daga nan suka kawo da kara ofishin ‘yan sanda.

    Ya ce laifin da Onyega ya aikata ya saba wa dokar hukunta masu aikata miyagun aiyukka ta shekara 2015 ta jihar Legas.

    Bisa ga sashe 137 na dokar hukuncin duk wanda aka kama da laifin fyade shine daurin rai da rai a kurkuku.

    An ceto mutane 5, biyu sun makale a wani gini mai hawa biyu a Abuja

    Rundunar hadin gwiwa ta jami’an tsaron farin kaya ta Najeriya da jami’an tsaron farin kaya da na ‘yan sandan Najeriya da wasu mazauna yankin sun ceto mutane biyar da abin ya rutsa da su.

    Gidan bene mai hawa biyu da ke Kubwa a unguwar da ke cikin karamar hukumar Abuja a babban birnin tarayya Abuja ya ruguje a daren ranar Alhamis. Har ila yau, ginin yana dauke da kantin sayar da kayayyaki.

    Daya daga cikin wadanda aka ceto, Hafeez Olayinka, wanda ya zanta da PUNCH, ya tabbatar da cewa ginin ya ruguje ne a daren ranar Alhamis da misalin karfe 11:30 na dare, amma an ceto su ne da sanyin safiyar yau Juma’a, kuma mun samu nasarar ceto su. aka kaita asibiti.

    Ya lura da cewa ya isa ginin da ya ruguje ne a ranar Litinin domin gyara wasu abubuwa a cikin ginin.

    Olayinka ya ce, “Mun shiga tarko tun daren Alhamis. Na zo nan tun ranar Litinin don gyara wasu abubuwa a cikin ginin.

    “Da misalin karfe 11:30 na daren ranar Alhamis, mun lura cewa ginin na rugujewa, sai muka yi kokarin tserewa. Amma an ceto mu biyar a safiyar yau, kuma sun kai mu asibiti.

    Share. Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr WhatsApp Email

    Related Posts

    Yadda Kanin Miji Ya Dirkawa Amaryar Yayansa Ciki A Nasarawa

    November 19, 2022

    Sati Biyu Kacal Da Yin Aure Amarya Ta Bukaci Ango Ya Saketa Saboda Baya Iya Gamsar Da Ita A Kan Gado

    November 18, 2022

    Yadda Ake Kwalliyar Maida Tsohuwa Yarinya

    November 7, 2022

    Lokuta Da Yawa Maza Yan Iska Sunfi Iya Soyayya Wata Budurwa Ta Kira Ruwa

    November 5, 2022

    Yadda Ango Yayi Dawowar Bazata Ya Kama Matarsa Da Babban Abokinsa Suna Cin Amanarsa

    November 4, 2022

    Bidiyon Hira Da Matar Da Take Auren Maza Biyu Kuma Suke Kwana Kan Gado Daya

    November 3, 2022
    Add A Comment

    Leave A Reply Cancel Reply

    Check Also

    Ya Kamata Kusan Da Wadannan Tsaruka Na Tallafi Da Ake Bawa Yan Nigeria

    January 27, 2023

    FG Begins SMEDAN ₦1.5m Loan – Application Portal

    January 20, 2023

    How to Obtain an Ecowas ePassport as a Holder of a Nigerian Passport

    January 20, 2023

    Easy Way to Apply for a Visa in Nigeria

    January 20, 2023

    Apply 2023 Microfinance Bank Kaduna Recruitment

    January 20, 2023
    • About Us
    • Contact Us
    • Disclaimer
    • Privacy Policy
    • Terms & Conditions
    Copyright © 2023 AMIHAD.COM | All Right Reserved.

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.