Close Menu
    AMIHAD.COM
    • Admission
    • Education
    • Finance
    • Scholarship
    • Tech
    • Visa
    AMIHAD.COM
    News

    Yadda Aka Kama Wani Yana Lalata Da Yar Uwansa A Jihar Kebbi

    Lucky MurakamiBy Lucky MurakamiOctober 6, 2022No Comments2 Mins Read

    Rundunar ‘yansandan Jihar Kebbi ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da aikata fyade a jihar.

    Kwamishinan ‘yansanda, Ahmad Magaji-Kontagora ne, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai.

    Ya ce wadanda ake zargin sun yi wa wata yarinya ‘yar shekara takwas fyade yayin da dayan kuma ya yi wa ‘yar uwarsa mara hankali fyade.

    “Wani Danjuma Tanko mai shekaru 30 da ke kauyen Zariya Kala-Kala, a karamar hukumar Koko/Besse, ya dauki wata yarinya ‘yar shekara takwas da ta ke siyar da wainar wake a gidan wani Umaru Dauda, ​​inda ya yi lalata da ita da karfin tsiga. Ya sadu da ita ya ba ta N200.

    “Wanda ake zargin ya bai wa Dauda N200 saboda amfani da dakinsa wajen aikata lalatar.”

    Kwamishinan ya tabbatar da cewa a ranar 16 ga watan Satumba, da misalin karfe 1:00 na rana, wanda ake zargin, ya dauki ‘yar uwarsa marar hankali ya kai ta magudanar ruwa tare da yin lalata da ita ta karfi.

    Ya kuma bayyana cewa, fyade na biyu da ake zargin wani Bashir Ibrahim na garin Kangiwa ne ya aikata a ranar 26 ga watan Satumba, inda ya kara da cewa za a gurfanar da wanda ake zargin a kotu bayan yin bincike.

    Magaji-Kontagora, ya shawarci ’yan Nijeriya da su rika sanya ido a kan wuraren da suke kewaye da su domin dakile aukuwar irin wannan lamari tare da taimaka wa rundunar da bayanai masu amfani kan wadanda ake zargi.

    Related Posts

    Tofah Bayan Ganin Bidiyon Tinubu Yana Motsa Jiki, Malmai Sun Fara Zazzago Martani

    January 11, 2024

    Yadda Wata Matar Aure Ta Kama Mijinta Yana Cin Amanarta Ba Kunya Ba Tsoron Allah

    December 25, 2022

    Karshen Duniya Yazo: Yadda Dalibi Ya Dirkawa Malamarsa Ciki

    December 12, 2022

    Wani Dalibi Ya Kashe Kansa Saboda Ya Kasa Mallakar Wayar Naira Dubu Hamsin

    November 27, 2022

    An Kama Likitan Bogi Daya Dirkawa Yan Mata Hudu Ciki

    November 26, 2022

    Yadda Mahaifiyar Budurwa Tasa Saurayi Ya Dirkawa ‘Yarta Ciki

    November 25, 2022
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    • About Us
    • Contact Us
    • Disclaimer
    • Privacy Policy
    • Terms & Conditions
    Copyright © 2025 AMIHAD.COM | All Right Reserved.

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.