Close Menu
    AMIHAD.COM
    • Admission
    • Education
    • Finance
    • Scholarship
    • Tech
    • Visa
    AMIHAD.COM
    News

    Yadda Aka Yi Wa Bankuna 3 Fashi A Rana Daya

    Lucky MurakamiBy Lucky MurakamiSeptember 7, 2022No Comments2 Mins Read

    Wani rahoto da muke samu wanda majiyar amihad.com ta tabbatar ’Yan fashi dauke da manyan makamai sun kutsa cikin bankuna uku da tsakar rana tare da yin awon gaba da kudaden da ba a tantance yawansu ba a Jihar Kogi.

    Kamar majiryarmu jaridar Aminiya ta rawaito, a ranar Talata ’yan fashi a motoci da babura suka kutsa cikin rassan bankunan Zenith da UBA da kuma First Bank a garin Ankpa da ke jihar da misalin karfe 2 na rana.

    Bayan fashin, “Sun zaburi ababen yawansu suka bi ta Titin Okpo, amma babu wanda ya iya fitowa saboda yadda suke ta harbi kan mai uwa da wabi,” in ji wani ganau.

    Shaidu sun ce ’yan fashin sun fara shiga bankin UBA ne, daga nan suka kutsa Zenith sannan suka shiga FirstBank.

    Ganau sun shaida wa wakilinmu cewa bayan maharan sun yi wa bankunan fashi; sun shafe kusan awa guda suna bin masu harkar cirar kudi na POS da ke kusa da bankunan suna yi musu fashi kafin su wuce suna harbe-harbe.

    Zuwa lokacin hada wannan rahoto babu tabbacin ko akwai wanda ya rasa ransa a harin.

    Amma wani mazaunin garin na Ankpa, Ahmed, ya ce, “Ba abin mamaki ba ne idan aka samu asarar rai.”

    Wani dan garin ya ce bayan tafiyar ’yan fashin, an ayarin rundunar hadin gwiwa ta jami’an tsaro sun nufi yankin da abin ya faru.

    Har aka kammala hada wannan rahoto dai Kakakin ’yan sanda na Jihar Kogi, SP William Aya, bai amsa rubutaccen sako da muka tura masa na neman karin bayani ba.

    Related Posts

    Tofah Bayan Ganin Bidiyon Tinubu Yana Motsa Jiki, Malmai Sun Fara Zazzago Martani

    January 11, 2024

    Yadda Wata Matar Aure Ta Kama Mijinta Yana Cin Amanarta Ba Kunya Ba Tsoron Allah

    December 25, 2022

    Karshen Duniya Yazo: Yadda Dalibi Ya Dirkawa Malamarsa Ciki

    December 12, 2022

    Wani Dalibi Ya Kashe Kansa Saboda Ya Kasa Mallakar Wayar Naira Dubu Hamsin

    November 27, 2022

    An Kama Likitan Bogi Daya Dirkawa Yan Mata Hudu Ciki

    November 26, 2022

    Yadda Mahaifiyar Budurwa Tasa Saurayi Ya Dirkawa ‘Yarta Ciki

    November 25, 2022
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    • About Us
    • Contact Us
    • Disclaimer
    • Privacy Policy
    • Terms & Conditions
    Copyright © 2025 AMIHAD.COM | All Right Reserved.

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.