Mace duk tsufanta ba ta son a ce da ita ta tsufa. Kullum tana so a rika ganinta kamar yarinya ko budurwa.
Koda biki za ta sai a ga tana kokarin ta ga ta fi ’yan mata ado da takalma ko riga da kuma kwalliya.
Don haka ne a yau na kawo muku yadda za a magance irin yadda za a cancada kwalliyar ‘mai da tsohuwa yarinya.’
Kwalliyar ido Babban kuskuren da mata suke yi idan sun zo yin kwalliya wa idanunsu shi ne, maimakon su sa kwalli ko gazal wa idon kawai, sai su hada bakin kwallin a fatar saman idanu.
Idan mace ta dan manyanta bai kamata ta rika irin wannan kwalliyar ba. Sai dai ta zabi daya.
Ko ta sanya gazal a ido ta bar saman idon ko kuma ta shafa eye shadow a fatar ido ta bar idon ba kwalli.
Yin duka biyu na sa ta yi kama da dodo. Gyaran fatar fuska da jiki Idan shekaru suka ja, lallai ne a kula da fatar jiki fiye da kwalliyar da za a yi a fuska. Sirrin yin hakan shi ne, ana son fitar mace ta zama kamar ba ta yi wata kwalliya ba.
Don haka, ya kamata a shafa hodar fandesho daidai da yanayin fatar fuska don boye tattarewar fuska da kuma tsufa. Idan akwai kuraje a fatar jiki ko fuska, za a iya amfani da man concealer a hada da hodar fandesho don boye wannan tabo ko kurarrajin fata.
Kada a manta amfani da launin da ya dace da fata wajen sanya hodar fandesho. Baki Ba lallai ba ne a nemi launi mai haske sosai wajen sa jambaki. Koda ja ce za a iya a sa jan da bai cika haske ba.
Ko kuma man baki kadai ya wadatar. Idan aka gwada wannan kwalliyar lallai za a ga tsohuwa ta koma yarinya.
[…] baku manta ba kwanakin baya Adam mijin momee ya zargi Hamisu breaker da hura mata kunne momee. Tana da aure ya saka ta a faifan bidiyo na waka hamisu breaker ya […]