• Sat. Jul 20th, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Yadda Alkali Ya Biyawa Wani Matashi Sadakin Naira Dubu Dari Dan Ya Auri Masoyiyar Sa

ByLucky Murakami

Aug 31, 2022

Mahaifiyar wata budurwa takai karar wani matashi kotu akan ya auri ‘yarta inda alkalin kotun yayi alkawarin zai biya.

Jaridar Premiumtimes ta rawaito cewa Alkalin kotun shari’a dake jihar Kaduna Salisu Abubakar-Tureta ya biya wa wani matashi mai suna Salilu Salele sadakin aure naira N100,000 ya auri masoyiyar sa Bilkisu Lawal.

Alkali Abubakar-Tureta ya bayyana wa Salele da ya je ya yi nazari akan tayin da ya yi masa sannan ya daga shari’ar zuwa ranar 6 ga Satumba.

Dama mahaifiyar Bilikisu, Rayila Lawal ta kai karar Salele kotu inda take bukatan kotu ta tilasta Salele ya auri ‘yarta Bilkisu idan har ya tabbatar yana kaunar ta ko Kuma ya rabu da ita idan har ya san bai shirya aure ba.

“A wuri daya muke zama sannan kulum yana zuwa wajen Bilkisu ba tare da ya nemi izinin mu iyayenta ba.

“Na yi wa mahaifiyar Salele bayanin abin dake faruwa amma ta ce danta bai shirya aure ba.

“Bayan haka sai Salele ya daina zuwa wurin Bilikisu a gida amma sai yana kiranta ta wayan suna haduwa a wani wuri.

“Na kawo karansa ne saboda bana so ya lalata tarbiyar da na bai wa ‘yata.

Raliya ta ce a shirye take ta aura wa Salele Bilkisu idan har ya shirya aure.

Salele ya bayyana a kotun cewa yana kaunar Bilkisu sai dai bai shirya aure ba sai nan da shekaru biyu masu zuwa.

“Ni dalibin daya daga cikin jami’o’in kasar nan ne amma ba zan so na raba hankali na biyu ba saboda aure ba.

“Bani da kudin biyan sadakin auren ta sannan har yanzu Ina zama tare da iyaye na ne. Inji Salele.

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *