• Sat. Jun 22nd, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Yadda Amarya Ta Mutu Ranar Daurin Aurenta

ByLucky Murakami

Oct 29, 2022

Wata Amarya mai suna Hannatu Yahaya, ta rasu ranar da aka daura mata aure. An daura wa Hannatu aure tare da Isyaka Yusuf, a Kawon Maigari da ke Kano, ranar Juma’a 28 ga watan Oktoba, amma sai ta mutu a wannan ranar a Kano.

Yan uwanta sun ce bayan an daura aurenta, lokacin da aka shirya domin a kai ta gidan mijinta, sai Hannatu ta fara yin ababe masu ban mamaki. Ya ce ta fara lalata kayakin gidansu tare da fizge-fizge har sai da aka kamata aka rike.

Daga bisani an kai ta Asibiti inda aka tabbatar da mutuwarta.

Kazalika wani dan uwanta ya ce, mako biyu da suka gabata, hannatu ta yi fama da cutar gyambon ciki wato ulcer, kuma sakamakon haka aka kwantar da ita a asibiti har tsawon mako daya. An sallameta ranar Alhamis 25 ga watan Nuwamba daga Asibiti.

Ya ce ta sake kamuwa da rashin lafiya kuma, amma ta sha magunguna. Ya ce lamarin jikinta ya rikice ne ranar da aka daura aurenta, kuma lokacin da ake kokarin kai ta gidan mijinta.

Allah ya jikanta.

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *