Wani ango ya tsere ya bar wurin taron bikin aurensu babu shiri bayan da ya gano amaryarsa na da ’ya’ya hudu a waje.
A cikin hoton bidiyon taron bikin da aka yada a kafafen sadarwa na zamani, an ga wasu kawaye da amaryar suna rarrashin ta yayin da take sharbar kuka kan abin da ya faru.
An ce ana tsaka da daurin aure ne amarya ta shaida wa ango cewa tana da ’ya’ya hudu a waje.
Shi kuma da jin hakan, sai ya fice a guje ya bar ta tare da mahalarta daurin aure, a wurin taron da ba a bayyana ba.
Wannan al’amari ya haifar da rudani a tsakanin mahalarta taron, inda wasunsu suka shiga tantamar anya angon ya san da matsayin amaryar kafin auren kuwa?
Da yake tsokaci kan batun, angon ya karyata amaryar cewa ba ta sanar da shi komai game da yaran ba.
Masu amfani da kafafen sadarwa na zamani na ci gaba da tafka muhawara a kan wannan batu, inda wasun ke kallon lamarin da ta-leko-ta-koma wa amaryar.