• Sat. Jul 20th, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Yadda Ango Ya Shigo Daki Ya Kama Matarsa Tana Lalata Da Tsohon Saurayinta

ByLucky Murakami

Oct 23, 2022

Abinda ya faru bayan wani magidanci ya kama matarsa tare da tsohon saurayinta a kan gadonsa.

Wani magidanci mai shekaru 51 ya jefa iyalinsa cikin damuwa bayan ya kwankwadi wani maganin kashe kwari mai karfin gaske (sniper) saboda ya dawo daga aiki ya kama matarsa turmi da tabarya ta na lalata da tsohon saurayinta.

Magidancin, dan asalin kasar Zimbabwe, ya kashe matar ta sa sannan ya gaggauta shan maganin kwari.

Rahotanni sun bayyana cewa magidancin mai suna Simbarashe Chidaushe, mazaunin garin Gokwe, ya yi amfani da gatari wajen kashe matar bayan ya kama ta dumu-dumu ta na cin amanarsa da wani mutumin, sannan ya yi kokarin kashe kansa ta hanyar shan maganin kwari.

Yanzu haka Chidaushe na can asibitin yankin Gokwe inda likitoci ke kokarin ceto lafiyarsa bisa ‘sa idon’ jami’an ‘yan sanda da ke gadin dakin da aka kwantar da shi.

Majiyar mu ta bayyana cewa Chidaushe, dan asalin kauyen Njele, ya kama matarsa, Chiedza Mpofu, na saduwa da saurayinta bayan ya yi wata dawowar bazata daga wurin aikinsa da ke wani gari kusa da garin Gokwe da yake zaune da iyalinsa.

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *