Close Menu
    AMIHAD.COM
    • Admission
    • Education
    • Finance
    • Scholarship
    • Tech
    • Visa
    AMIHAD.COM
    News

    Yadda Bankin Duniya Ya Dauki Nauyin Karatun Yarinyar Nan Me Baiwar Lissafi A Kano

    Lucky MurakamiBy Lucky MurakamiAugust 4, 2022No Comments2 Mins Read

    Labarin da muke samu shine Saratu Garba, yarinyar nan mai shekara 11 mai baiwar lissafi a kauyen Gwadayi na karamar hukumar Gaya a jihar Kano, ta sami tallafin karatu daga Bankin Duniya.

    Saratu ta samu tallafin ne a karkashin shirin tallafawa mata don su yi ilimi (AGILE), wanda Bankin ke daukar nauyi a jihar Kano.

    Amihad.com ta samo wannan labari ta hanun Malam Aliyu Musa, Jami’i Yada Labarai na shirin wanda shine ya bayyana haka ga Kamfanin Dillacin Labarai na Najeriya (NAN) a ranar Laraba.

    Malam Yusuf wanda kuma shi ne Mataimakin Daraktan yada labarai na Ma’aikatar Ilimi ta jihar Kano ya ce, ofishin kula da shirin na Bankin Duniya a jihar Kano ya bayar da umarni a zakulo yarinyar nan a kuma sa ta a makaranta.

    “Sai a ka yi sa a, masu kula da shirin ilimin mata na AGILE na tsaka da ziyara zuwa masarautu biyar na jihar Kano don neman hadin kan sarakuna kan batun ilimin mata a jihar,” inji shi.

    A yayin ziyararsu a masarautar Gaya ne jami’an suka yi wa Sarki bayanin yarinyar da kuma aniyarsu ta daukar nauyin karatunta, sai Sarkin na Gaya ya sa aka zo da yarinyar da kuma iyayenta har gabansu.

    Nan take wakilin a Ma’aikatar Ilimi ta jihar Kano, Malam Haruna Mohammed Pandau, ya ba Saratu kayan makaranta da jakar makaranta da kuma wasu kayayyakin karatu.

    Shi kuma Ado Tafida Zango, mai kula da shirin AGILE a jihar, ya ba ta Naira 20,000 daga aljihunsa don taimaka wa karatun nata.

    Muna fatan Allah ya kara bawa yaranmu nasara.

    Related Posts

    Tofah Bayan Ganin Bidiyon Tinubu Yana Motsa Jiki, Malmai Sun Fara Zazzago Martani

    January 11, 2024

    Yadda Wata Matar Aure Ta Kama Mijinta Yana Cin Amanarta Ba Kunya Ba Tsoron Allah

    December 25, 2022

    Karshen Duniya Yazo: Yadda Dalibi Ya Dirkawa Malamarsa Ciki

    December 12, 2022

    Wani Dalibi Ya Kashe Kansa Saboda Ya Kasa Mallakar Wayar Naira Dubu Hamsin

    November 27, 2022

    An Kama Likitan Bogi Daya Dirkawa Yan Mata Hudu Ciki

    November 26, 2022

    Yadda Mahaifiyar Budurwa Tasa Saurayi Ya Dirkawa ‘Yarta Ciki

    November 25, 2022
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    • About Us
    • Contact Us
    • Disclaimer
    • Privacy Policy
    • Terms & Conditions
    Copyright © 2025 AMIHAD.COM | All Right Reserved.

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.