AMIHAD.COM
    • Admission
    • Education
    • Finance
    • Scholarship
    • Tech
    • Visa
    AMIHAD.COM
    Home » Yadda Bene Mai Hawa Uku Ya Rufta Da Mutane A Kano
    News

    Yadda Bene Mai Hawa Uku Ya Rufta Da Mutane A Kano

    Lucky MurakamiBy Lucky MurakamiAugust 31, 2022No Comments3 Mins Read
    Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr WhatsApp Email
    Share
    Facebook Twitter LinkedIn WhatsApp Pinterest Email

    Wani bene da ake tsakiyar gini mai hawa uku ya rufta kan mutanen da aka tabbatar su na da yawan gaske a Kano.

    Hatsarin ya faru a ranar Talata a kasuwar sayar da wayoyin GSM da ke kan titin Beirut Road da ke tsallaken Kasuwar Kantin Kwari.

    Labarin da muke samu kamar yadda jaridar Aminiya ta rawaito wani ganau da ya zanta da wakilinmu, ya ce ginin wanda ya rufta fiye da sa’a guda da ta gabata, har yanzu ba iya ceto wadanda suka makale a karkashin baraguzansa ba.

    Ya alakanta jinkirin da aka samu wajen ceto mutanen da rashin kayan aiki da za a iya yakice baraguzan ginin masu nauyin gaske.

    A cewarsa, an jiyo muryar daya daga cikin wadanda tsautsayin ya auku a kansu kuma har yana iya amsa wayarsa ta salula yayin da aka kira.

    “Yanzun nan muka kira layinsa kuma ya dauka. Sai dai ba shi da damar ceton kansa,” a cewar wani da lamarin ya faru a kan idonsa.

    Sai dai wani daga cikin wadanda nauyin ceto ya rataya a wuyansu, ya ce manyan motocin hakar kasa na kan hanyar zuwa kasuwar a yayin da ake ci gaba da kai komo na ganin an ceto wadanda suka makale.

    Wakilinmu ya ruwaito cewa, ya zuwa yanzu an ceto wasu mutum uku da tuni an yi gaggawar mika su asibiti.

    Wani daga cikin wadanda suke ba da gudunmawar aikin ceton ya ce, mutane da dama ciki har da mata da kananan yara suna makale a karkashin baraguzan gini, inda wasunsu ke kururuwar neman dauki.

    Ya ce duk da tarin mutane sun hallara a wurin tare da nuna alhini, babu abin da za su iya aiwatarwa saboda babu wani dan Adam da zai iya dauke manyan baraguzan da suka danne mutanen.

    Kazalika, ya ce babbar motar da aka kawo domin aikin yakice manyan baraguzan ita kanta lamarin ya fi karfinta.

    “Wasu ’yan mata masu sayar da dafaffen kawai da mata masu sayar da abinci sun makale a karkashin ginin.

    “Sai da muka haka rami sannan muka iya ceto mutanen uku su ma da kyar. Sauran suna karkashin ginin amma mun kasa gano hakikanin wurin da suke sai dai kawai muryoyinsu muke ji.”

    A cewarsa, tun ba yanzu ba suka gano ginin benen ya fara tsagewa, lamarin da ya sanya suka ankarar da masu aikin kwangilar amma suka ce da su babu abin da zai faru.

    Majiryarmu Aminiya ta ruwaito cewa, daga cikin masu aikin ceton da suka hallara a wurin har da jamian Hukumar Kwana-Kwana, Hukumar Kiyaye Hadurra da ’Yan sanda da kuma jami’an Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa (SEMA).

    Da yake zantawa da wakilinmu, Sakataren SEMA, Dokta Salahe Jili, ya ce suna ci gaba da yin duk wata mai yiwuwa domin ceto wadanda lamarin ya rutsa da su.

    Share. Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr WhatsApp Email

    Related Posts

    Yadda Wata Matar Aure Ta Kama Mijinta Yana Cin Amanarta Ba Kunya Ba Tsoron Allah

    December 25, 2022

    Karshen Duniya Yazo: Yadda Dalibi Ya Dirkawa Malamarsa Ciki

    December 12, 2022

    Wani Dalibi Ya Kashe Kansa Saboda Ya Kasa Mallakar Wayar Naira Dubu Hamsin

    November 27, 2022

    An Kama Likitan Bogi Daya Dirkawa Yan Mata Hudu Ciki

    November 26, 2022

    Yadda Mahaifiyar Budurwa Tasa Saurayi Ya Dirkawa ‘Yarta Ciki

    November 25, 2022

    Yadda Aka Kama Malamin Addini Yana Lalata Da Yan Mata Biyu Yan Uwan Juna

    November 23, 2022
    Add A Comment

    Leave A Reply Cancel Reply

    Check Also

    Ya Kamata Kusan Da Wadannan Tsaruka Na Tallafi Da Ake Bawa Yan Nigeria

    January 27, 2023

    FG Begins SMEDAN ₦1.5m Loan – Application Portal

    January 20, 2023

    How to Obtain an Ecowas ePassport as a Holder of a Nigerian Passport

    January 20, 2023

    Easy Way to Apply for a Visa in Nigeria

    January 20, 2023

    Apply 2023 Microfinance Bank Kaduna Recruitment

    January 20, 2023
    • About Us
    • Contact Us
    • Disclaimer
    • Privacy Policy
    • Terms & Conditions
    Copyright © 2023 AMIHAD.COM | All Right Reserved.

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.