• Mon. Jun 17th, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Yadda Budurwa Ta Damfari Mai Wasan Barkwanci Naira Dubu 800 Da Sunan Kudin Haya

ByLucky Murakami

Sep 27, 2022

Yadda budurwata Ta dinga damfarata kudi domin biyan kudin haya 800,000.

Dan wasan barkwancin nan, Michael Sani Amanesi, Wanda akafi Sani da MC Lively ya bayyana yadda tsohuwar budurwarsa ta dinga damfararsa kudi da Sunan tanada juna biyu domin tasamu ta biya kudin haya 800,000.

Wannan ya kasance sakamakon rudanin daya shiga na Shekarar 2021 daya kasance a Ciki, wanda ya bayyana cewa baiyima budurwar ‘yar Shekara 21 juna biyu ba, Kuma ya ganota bayan yace taje a Zubar da Cikin.

Lokacin da yake magana da yan jarida, Chude Jideonwo, dan Shakara 30 ya gabatar da cewa dukkan labarin karyane, Wanda yarinyar ta kirkira domin ta karbi kudi daga gurinsa.

Kamar yadda yace, ta kasance a koda yaushe tanason alakar banza ta shiga tsakininsu, amma naki yadda.

Ana haka naga wani abu a tartare da ita, Ina son waka ina kuma son mutane Wanda suka iya waka.

Dan haka ta kirani tace mun tanason in taimaka mata in biya mata kudin hayar gidanta, ina tunanin kudin sun kai naira 800,000, banda kudin dan haka na shareta.

Wata rana ta yaudareni da alakar banza kuma na biyeta, bayan Sati ukku da faruwar hakan ta kirani ta fadamun tana da juna biyu.

Abunda ya faru ya riga ya faru dan haka mikikeso yanzu? Tace tana son ta fitar dashi Saboda idan iyayenta Suka gane Kasheta Zasuyi.

Ni bansan cewa idan mutum ya cema yanada juna biyu abu na farko da ake fara tambayarsa Shine Shedar gwajin Ciki na asibiti ba.

Amma lokacin Dana fara gane karya take Saboda kullum Cikin tambayata Kudi take.”

Ya kara da cewa, “kuma wata rana ta tambayeni zata wani guri kuma ranar ta kasance asabar, nace mata tayi hakuri amma banda kudi, tayi fushi dan haka da Sauri na tura mata kudin.

Da misalin karfe 12 na rana na tarar da dogon Sakon ta yana cewa bataje gurin likitocin ba Saboda duk kulle Suke yau asabar, tace Zataje ranar litinin, kwata kwata ban gamsu da maganar taba dan haka ban maida mata martani ba.

Ranar litinin, na tarar da dogon Sakonta tana cewa kasancewa dai inada sokonninka da sakon muryanka, da bidiyoyinka, dan haka zan watsa su duniya(posting) idan baka maidomun martani ba.

Wannan Shine tsarinki duk dadewar, nafada mata nayi matukar mamaki, kuma ban tsorata ba.

Idan kinaso ki watsa a ko inane kije ki watsa. Ban dauka yaudara bace nayi tunanin kawai dan ta tsoratani amma daga karshe na gane ba tada wani juna biyu da fari ma, kawai tanason ta kwaci naira 800,000 da takeso ta biya haya.

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *