Wata budurwa a jihar Kano ta gudu motar saurayinta bayan yaje saya mata shawarma a wata anguwa wanda hakan ya jawo cece-kuce. Amma dai ku saurari gaskiyar abinda yafaru.
A wani labari da muka samu rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wata budurwa mai suna Ilham Kabir Karaye da ake zarginta da sace motar saurayinta bayan da ya fita sayo mata Shawarma a unguwar Kofar Famfo, da ke kan titin Jami’ar Bayero a jihar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar da haka ga manema labarai da yammacin yau Litinin.
A cewarsa sun samu rahoto daga wajen wanda aka dauke wa motar a ranar 12 ga Yulin 2022, inda ya kai korafin cewa an sace masa mota.
Bayan da ‘yan sandan suka kama ta, budurwar Ilham, ta bayyana cewa tana bin saurayin nata kudi ne N150,000 kuma tana ganin ba zai bata ba hakan yasa ta yanke shawarar dauke masa mota.
Sai dai a cewar saurayin, sun yi waya ne kuma suka hadu a hauren wanki, inda daga nan tace tana jin yunwa kuma shawarma take son ci, sai dai fitarsa ke da wuya domin siyo wa ya dawo ya tarar da motar ta yi batan-dabo.
Ilham dai ta bayyana wa ‘yan sanda cewa wani saurayinta ta kirawo ya tuka motar ya tafi da ita gida ya ajiye mata kuma ta dauki motar ne domin kudin da take bin sa.
Tuni dai aka kama Ilham da saurayin nata da ya tuka motar domin ci gaba da bincike.