Wata mata ta shiga hannu bayan ta caka wa masoyinta kwalba tare da aika shi lahira saboda sabanin da suka samu.
Matar, wadda ’ya’yanta uku, ta caka wa saurayin nata mai shekara 44 kwalba ne a wuya da kuma bayansa, wanda ya yi sanadiyar mutuwarsa a garin Benin, Jihar Edo.
Takaddamar ta faro ne bayan saurayin nata, wanda magidanci ne mai ’ya’ya uku, ya bi ta a guje da bayan ya yi arba da ita a gidan wani wanda yake zargin shi ma saurayinta ne.
Ita kuma mai shekara 26, ta dauki kwalba ta daba masa a baya da wuyansa, wanda hakan ya yi ajalinsa.
Aminiya ta yi karo matar, mai shekara 26, bayan ’yan sanda sun cika hannu da ita, sun buga mata anka, za su tafi da ita.
Wadda ake zargin ta shaida wa wakilinmu cewa, “Da ya gan ni da wani mutum ne ya bi ni har gidan mutumin zai yi fada da ni. Amma ba a gidan nake zama ba, na je ziyara ne.”
Kakakin ’yan sandan Jihar Edo, SP Chidi Nwabuzor, ya ce jami’an rundunar sun iske gawar mutumin, wanda direban bas din haya ne kwance a cikin jini, bayan faruwar lamarin.
Ya ce an tisa keyar matar zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka domin tsananta bincike a kanta, kafin a gurfanar da ita a kotu.