• Sun. Dec 8th, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Yadda Daliban Sakandare Sukayi Zanga-zanga Saboda Tsarin Raba Maza Da Mata A Bauchi

ByLucky Murakami

Feb 27, 2024

Bamu Amince da Tsarin Raba Maza Da Mata ba – Zanga-Zangar Daliban Jihar Bauchi

 

A ranar Litinin 26/09/2022, Rana ce da aka koma makarantu a Jihar Bauchi kamar yanda hukumomi suka bada daman haka.

Jim kadan bayan komawa Makarantun, wasu daga cikin daliban sun mamaye manyan tituna a cikin garin garin Bauchi, suna bayyana wa Gwabnati rashin amincewar su da tsarin raba maza da mata da Gwamnatin jihar Bauchi tayi.

Na samu jin ta bakin wani ɗalibi wanda yaso na dakaye sunan shi, ko meye dalilin wannan zanga-zanga da sukeyi, ya bayyana mani cewa, lallai sunayi ne sabida rashin adalcin da aka musu na rabasu da abokan karatun su mata kenan, dan ya zama wajibi gwamnati ta duba wannan Lamari.

Idan ba a manta ba Gwamnatin jihar Bauchi dai, ta bijiro da tsarin raba Maza da Mata ne ta bakin Komishinan ilimi na jihar, Dr Aliyu Dilde, da nufin rage baɗala da yake afkuwa a tsakanin ɗaliban.

Tuni dai Jami’an ‘yan Sanda suka tarwatsa gangamin daliban, daga karshe kowa ya gudu izuwa gidan su.

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *