Hukumar ‘yan sanda reshen jihar Enugu tace ta damƙe wasu mutum Shida da take zargi da tuɓe wata mata tsirara kana suka ci zarafinta a jihar.
Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar yan sandan jihar, Daniel Ndukwe, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Jumu’a, kamar yadda Jaridar Premium Times ta ruwaito.
Lamarin ya faru ne a ranar 27 ga watan Oktoba, 2022 a yankin Agunese, Afam-Mmaku, wani kauye a ƙaramar hukumar Awgu, jihar Enugu.
Matasan ƙauyem sun zargi matar mai suna, Anthonia Okonkwo, da gurbata musu wuri mai tsarki ta hanyar noman dodon koɗi a kusa da wurin. Zargin da matar ta musanta.
Misis Okonkwo, tace kowa ya santa tana sana’ar noma dodunan koɗi a ƙauyen kuma ta siyarwa mutane tsawon lokaci domin ta kula da yaranta huɗu tun bayan mutuwar majinta shekaru 13 da suka shuɗe. Yadda lamarin ya faru.
Yadda lamarin ya faru
Da take labarta yadda lamarin ya auku, Okonkwo tace wata rana tana zaune a cikin gida sai kawai ta jiyo cece-kuce a waje, ba zato wasu matasa suka kutsa kai suka jawota waje ba tare da sauraronta ba.
A cewarta, nan take matasan suka fara lakaɗa mata duka da makamai da Bulalu, suka tuɓe mata kaya, suka ɗaura mata ganyen dabino a ƙugu da wuya, alamar dake nuna ta aikata saɓo a yankin.
Wane mataki aka ɗauka?
Kakakin yan sandan yace tuni jami’an tsaro sun yi ram da mutum shida daga cikin matasan da suka jagoranci aikata wannan ɗanyen aiki, kamar yadda Sahara Reporters ta ruwaito.
Ya kuma ambaci sunayensu da Maduabuchi Madueke, Obioma Nwangene, da Stan Okoro, da ake zargi ta jan ragamar sauran, sai kuma Samuel Anikene, Chukwuebuka Agu, da Jonathan Nwangene, da suke biye musu.
“Ana cigaba da bincike da nufin lalubo sauran masu hannu a lamarin, ” Inji DSP Ndukwe. Yace a binciken da dakaru suka gudanar, waɗanda ake zargin sun haɗa da ɗan uwan matar suka lakaɗa masa duka yayin da ya yi yunkurin taimaka mata, sun ji masa raunuka.