Wani bidiyo da yake yawo a shafukan sada zumunta na karamar yarinya yar TikTok tana tambayar jaruman kannywood data hadu dasu a kasar dubai ya jawo cece-kuce.
Yarinyar dai yar kasar Pakistan ce inda tayi musu tambayoyi da yaren turanci su kuma suna bata amsa, wanda hakan yasa mutane suke ta surutu akan yanayin yadda suka bata amsar.
Amihad.com ta gano cewa wadannan jarumai da suka bayyana a cikkin wannan bidiyo sun hada da; Maryam Yahaya, Momee Gombe, Minal Ahmad, da kuma Maryam. Sai ita yarinyar me yarinyar me tambayar sunanta Rumaisa yar kasar Pakistan.
Yarinyar dai ta tambayesu daga wace kasar suke inda suka fada fada daga Nigeria, sannan ta tambayesu sunayensu suka fada daya bayan daya.
Sai dai hakan yabar baya da kura inda mutane suketa raha da tsokanar yadda su jaruman suke bata amsa musamman jaruman Momee Gombe wai ba abinda take cewa sai; “Wow, wow, wow” kamar jiniya.
Sannan acikin bidiyon sn tambayi Maryam Yahaya yasunan ta da turanci sai dai ta gaza gane me ake nufi da hausa.
Abin Lura: Bamuyi wannan sharhi dan muci mutuncin wani ba saboda turanci yare ne kuma ba abun kunya bane ace mutum yayi kuskure ko kuma ace bai iya ba, saboda da yawa daga cikin masu martanin bazasu iya yin abinda wannan jarumai sukayi ba.
Hakika sunyi kokari matuka tunda duk cikinsu turanci ba yarensu bane, sai dai mutane da dama suna jinjinawa jaruma Minal Ahmad wanda itace tafiyi yin turancin dakyau a cikin jaruman.
Domin kallon wannan bidiyon ku dannan rubutun dake kasa:
Yadda Karamar Yarinya Ta Kunyata Jaruman Kannywood
In baku manta ba Jarumar Kannywood Momee Gombe Ta Saki Wasu Zafafan Hotunan Ta a Kasar Dubai Na Yawon Shakatawa Tareda Bude Ido.
Wannan Hotuna da Jaruma Momee Gombe Ta Saki Sunyi Matukar Burge Masoyan Ta Inda Sukayi Ta Yi Mata’ Fatan Al’kairi Akan Allah Uban’giji Subhanahu Wata Ala Ya’bata Miji Na Gari.
Babu Shakka Wannan Ita’ Ce Addu’ar da Masoyan Jaruma Momee Gombe Sukafi Yi Mata’ Domin Kuwa Babu Shakka Aure Shine Abunda Yafi Dacewa da Ko Wacce Mace.
Kuma Rayuwar Aure Rayuwa Ce Mai Kyau Sannan Aure Yana Gyara Rayuwar Mutun Musamman Ma Mace Yanzu Haka dai Muna Tafeda Wasu Daga Cikin Zafafan Hotunan Da Jaruma Momee Gombe Ta Saki.