Mahaifiyar budurwata ce ta nemi na yi wa ‘yarta ciki- Matashi
Matashin da ake zargin ya dirka wa budurwarsa ciki a jihar Oyo ya sanar da kotun da ke yi masu Shari’a a birnin Ibadan babban birnin jihar cewa mahaifiyar yarinyar ce ta roki ya yi wa ’yarta ciki kafin su yi aure.
Budurwa ce dai ta kai karar wannan matashi kotu don a raba tsakaninsu inda ta ce bayan ya yi mata ciki ya daina kula da ita da abin da ta haifa masa yadda ya kamata.
Matashin ya fada wa kotu cewa iyayen budurwar ne suka nuna cewa yar tasu ba za ta zauna da shi ba kuma a karshe aka rika hana shi ganin abin da budurwarsa ta haifa.