Dubun wani mai gadi ta cika bayan ya saci wayoyin hannu da kudinsu ya kai Naira miliyan daya da dubu dari biyar a kasuwar da yake aikin gadi.
An gurfanar mai gadin, mai shekaru 25 a gaban kotun Mai Shari’a O. A. Taiwo, na kotun da ke Ikeja Jihar Legas.
Ana tuhumar mai gadin da aikata laifuka hudu hadin baki, sata, fashi, da shiga wuri ba da izini ba amma ya musanta zarge-zargen.
Dan sanda mai gabatar da kara, Insfekta Raphael Donny, ya fada wa kotun cewa mai gadin tare da abokansa sun balla shagon wata ’yar kasuwa mai suna Winner Erebor a Ikeja a ranar 23 ga watan Yuni.
Daga nan suka sace wayoyi masu tsada na fiye da Naira Miliyan 1 da dubu dari biyar.
Hakan, a cewarsa, laifi ne da ya saba sashe na 307, 287, 309, da kuma 411 na kundin manyan laifukan Jihar Legas na 2015.
Alkalin ya bada belin mai gadin kan Naira dubu 100 da sharadin zai kawo wanda zai tsaya masa wanda kuma ya mallaki makamantansu.
Daga baya alkalin ya dage sauraron shari’ar zuwa ranar 15 ga watan Agusta mai kamawa.