• Sat. Jun 22nd, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Yadda Matan Aure Ke Tunzura Maza Zuwa Neman Mata A Waje

ByLucky Murakami

Aug 6, 2022

Bayanin da muke tafe dashi a yau shine yadda matan aure na wannan zamani suke ingiza mazajensu zuwa ga neman mata a waje duk da cewa suna da aure. Ko Kin San Da Kanki Za Ki Iya Tunzura Mijinki Ya Nemi Mata A Waje? Ku share zama domin karanta cikakken yadda abun yake kasancewa.

Wasu mazan suna fadawa neman mata ne, saboda sun auri ballagaza shashashar mace, wacce ba ta iya zaman aure ba, wacce ba ta iya kissa da tarairaya ba. Wacce ba ta san me rayuwar aure ya kunsa ba.
Ita dai kawai gatanan ne.

Babu kwalliya wa maigida, babu shafa turaruka masu kamshi da gyara fata, ba ta shafa mai wanda zai sa fatarta ta yi laushi, ba ta gyara gashin kanta, ba ta iya kwanciyar aure ba, ba ta iya shagwaba mai fisgar hankali ba, ba ta iya nuna kauna da soyayya ga miji ba.

Ba ta iya zama ta yin abubuwan da zai sa ka mijinta nishadantu ba. Ba ta iya magana ba, ba ta iya kallo ba. Ita dai ga ta nan ne kawai.

To kun ga mijinta baya samun abin da ya kamata ya samu a wurinta, mai ya yi saura? Sai ya je ya fara biye-biyen mata idan baya jin tsoron Allah. Kin ga kina daya daga cikin mutanen da suka ba shi gudunmuwa wurin jefa shi cikin wannan musiba ta neman mata.

Wani kuma yana fadawa neman mata ne, saboda mabukaci ne dayawa, ita kuma matar ba ta iya jure masa, har ya kai ga duk lokacin da zai neme ta sai an yi rigima, to a nan idan mijinki ya bukaci karin aure, kada ki hana shi, idan kuma kika yi masifa kika tayar masa da hankali, toh zai kuwa fada neman mata, kina zaune zai kawo miki tsarabar kanjamu har cikin dakinki. Don haka ki kyale shi ya yi aurensa don wani baya iya hakuri da mace daya.

Wata kuma ta iya kwalliya da kissa da tarairaiya da abinci da tsabta, ta iya kwanciya da komai, amma mijinta kuma manemin mata ne, to irin wannan sai a ce jarabawace, domin irin wannan mazan ko mata dari za a tara musu to ba zai hana idan sun ga wata su nema ba.

Domin su ba su dauki aure a bakin komai ba. Ki dage sosai da rokon Allah, sannan kada ki fasa abin da kike masa na kyautatawa, ki ci gaba da izinin Allah zai dai na wata rana.

Sannan ki rinka kokarin nuna masa illan yin hakan, misali: Ki ce wane idan ni kadai ba na isan ka ne, to ni babu damuwa ka karo wata, saboda ina ji maka tsoron cuta, kuma ina jiye maka tsoron kada abin da ka yi wa ‘ya’yan wasu a yi wa naka.

Magana za ki yi masa cikin nutsuwa da ladabi, a kuma lokacin da kika ga ya cancanta. Ki rinka yi masa magana cikin nutsuwa da sanyin murya. Kada ki nuna masa kina fushi, kada ki nuna bacin rai. In ma za ki yi kada ya wuce kina magana kina zubar masa da kwalla na nuna bakin ciki da damuwa.

Idan kina masa haka, kuma kina ribanya abubuwan da kike masa na kyautatawa. Da izinin Allah zai daina. Sannan Addu’a shi za ki dage da yi, babu dare babu rana, in Allah ya yarda za a wayi gari ya dai na ya dawo gare ki.

Maza ku ji tsoron Allah ku daina shiga hurumin da ba naku ba, zina haramunce har ranar alkiyama, ka tausaya wa kanka da matar ka, sannan ka tausaya wa zuri’arka, kada su taso a neme su, a lalata maka rayuwarsu. Na tabbatar ba za ka so hakan ba.

Allah ya kubutar da maza masu fama da wannan matsala.

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *