• Sat. Jun 22nd, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Yadda Miji Ya Kama Matarsa Dumu-Dumu Tana Saduwa Da Dan Uwansa

ByLucky Murakami

Nov 8, 2022

Wani Magidanci ɗan kasuwa, Justine Onu, ranar Litinin ya roki Kotun Kostumare dake zama a Jikwoyi, babban birnin tarayya Abuja, ta raba aurensa da Matarsa mai suna Joyce a takaice.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa Magidancin ya roki Kotu ta datse igiyoyin aurensu ne bisa zargin ya kamata dumu-dumu tana saduwa da ɗan uwansa.

Magidancin ya shaida wa Kotun cewa matarsa wata macece mai son yin jima’i da kowane mutun ta haɗu da kuma maganar gaskiya ya gaji da haƙuri da aurensu.

Mista Onu ya ƙara da gaya wa Kotu cewa ta kai ga ya kamu da ciwan hawan jini sakamakon halin mai ɗakinsa nA kwanciya da mutane barkatai.

Bugu da ƙari Magidancin ya ce matarsa wata macece da bata damu da alhakin dake kanta ba kuma bata kula da ‘ya’yan da Allah ya basu ko ta girka wa iyalansa abinci.

Shin matar da ake zargin ta amsa laifinta?

Amma a nata ɓangaren, matar da ake ƙara Joyce ta musanta baki ɗaya tuhume tuhumen da Mijinta ke mata a gaban alkalin Kotun, tace ba gaskiya bane.

Bayan sauraron kowane ɓangare, Alkalin Kotun mai shari’a Labaran Gusau, ya sanar da ɗage zaman zuwa ranar 8 ga watan Nuwamba, 2022 domin dawowa a ci gaba da zaman shari’ar, NAN ta ruwaito.

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *