Jami’an ‘yan sanda na kasar Rasha sun kama wani mutum mai suna Oleg Kirkunov mai shekaru 54 bisa laifin kashe matarsa da yayansa bayan ya kama su turmi da tabarya a wani dakin baki da ke gidansa.
Kirkunov ya shaidawa ‘yan sanda cewa yayansa, Evgeny ya kawo masa ziyara ne a gidansa inda suka ci abinci tare a birnin Ufa da ke Rasha.
Bayan sun gama cin abincin ne shi da matarsa Sukhanova suka amince Evgeny ya kwana a gidan kuma suka bashi makullin dakin baki domin ya kwanta kamar yadda Jaridar Punch ta ruwaito.
Oleg ya farka cikin dare saboda wani hayaniya da ya rika ji kuma a lokacin ne ya kura cewar matarsa ba ta kwance a gadonsu na aure.
Hakan ya sa ta tashi domin ya dubo matarsa kuma ya bincika mene hayaniyar da ya ke ji kwatsam sai ya ga yayansa da matansa suna saduwa a dakin baki.
Oleg wanda dama dan farauta ne ya yi maza ya dako bindigarsa ya harbe matarsa a yayin da ta ke kwance a kan gado, sannan ya juya ya harbe yayansa a lokacin yana kokarin sanya kaya kafin ya tsere.