• Sat. Jul 20th, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Yadda Sauro Yasa Wani Asarar Gilashin Mota Na Fiye Da Naira Dubu Dari Biyar

ByLucky Murakami

Aug 25, 2022

Lange-lange mai ramar keta. Ramamme firgita kato wannan wani bangare ne na kirarin da Bahaushe ke yi wa sauro.

Kuma sai ga shi sauron ya sa wani mazaunin Gabashin China mai suna Lou wanda ya fito daga garin Jiading a Lardin Zhejiang ya fasa gilashin motarsa a kokarinsa na kashe saurona ranar 11 ga Agustanan nan.

Lou ya yi amfani da hannunsa wajen kokarin kashe sauron da ke gaban gilashin motarsa kirar BMW, inda nan take gilashin ya fashe.

Shirin labarai na1818 huangjinyan na gidan talabijin Zhejiang Tb ne ya ruwaito haka a ranar Lahadin da t agabata.

Wani faifan bidiyo ya nuna yadda gilashin ya fashe ya kai gurbin hannu matashi kuma kudin gilashin ya kai kudin China Yuam 8,000 (kimanin Naira dubu 424 da 16 da kwabo 28). Lou ya ce, bai da laifi, illa matsalar daga gilashin ne.

Lou ya ajiye motar a gaban kantin gilashin mota na 4S bayan aukuwar lamarin.

Sai dai manajan kantin 4S Huang ya bayyana wa Zhejiang Tb cewa ba su taba samun irin wannan rahoto ba. Lou ya ce, bayan kwana uku da aukuwar lamarin kantin 4S ya canja gilashin kyauta bayan sun binciki motar inji Zhejiang Tb.

 

Subhanallah! An zargi kishiya da kisan amarya a ranar daurin ta a Sokoto

Labarin da muka samu daga majiyoyi da dama na nuni da cewa Allah ya karbi ran wata amarya a garin Sokoto dake a arewa maso yammacin Najeriya a ranar daurin auren ta.

Kamar dai yadda rahotannin na mu suka nuna amaryar ta fadi ne kasa kawai ta mutu a sakamakon wani matsanancin ciwon kai da ta ce tana fama da shi jim kadan bayan ai gama daurin aure kuma ana shirin tafiya kaita dakin ta.

Amihad.com ta samu cewa bayan an kammala daurin aure da safe, lokacin da ango ya turo motoci domin a daukar masa ita sai amarya ta bayyana masu cewa kanta na matsanancin ciwo sosai don haka a dakata.

Kamar ba za a dakata ba, amma ganin yadda ta matsa har da kuka akan ciwon kan nata sai aka bukaci a jira zuwa mintuna talatin a ga ya za a yi ko ciwon kan zai sassauta amma sai Allah ya karbi abun sa.

Tuni dai mutane suka fara zargin kishiyar da kisan inda suka ce daman can uwar gidan bata so auren ba.

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *