Wani dan Nijeriya Ya cinye malmalan tuwo 10 a cikin Sa’oi 10 a gasan cin abinci a Legas
Wani dan Najeriya ya bada mamaki, ganin yanda ya cinye malmalan tuwo har guda goma a cikin kankanin lokaci daga bisani ya samu kyautar 10, 000.
Matashin wanda ya doke abokin hamaiyarsa inda shikuma ya samu nasaran cinye malmala tara 9.
Wannan dai yafaru ne a wani gasan cin abinci a wani wuri a birnin legas, mutane da dama ne suka mamaye filin gasan kuma sun shiga mamakin yadda dan nijeriya ya cinye tulin tuwo a cikin mintuna kalilan.
Mista Tayin da ya kammala cinyewa, masoyan shi sunyi ihu tare da alfaharin dan uwansu dan nijeriya ne ya cinye gasan.