Ana zargin wani matashi da kashe abokinsa ta hanyar daba masa wuka a wuya saboda rikicin canji N300 da ya shiga tsakaninsu a jihar Legas.
Shaidu sun ce, lamarin ya faru ne bayan da matashin da abokin nasa suka hau babur din acaba daya daga wurin aiki zuwa gida a yankin Mushin.
Bayan da suka isa suka mika wa dan acaba kudinsa, inda ya karba kana ya mika musu Naira 300 a matsayin canji don su raba a tsakaninsu.
Mjaiyarmu ta ce a wajen rabon canjin ne rikici ya balle a tsakanin abokan, wanda daga bisani daya daga cikinsu ya zaro wuka ba tare da bata lokaci ba ya daba wa abokinsa a wuya.
“Ganin abin da ya aikata sai ya tsere, mu kuma muka yi kokarin kai shi asibiti amma rai ya yi halinsa a hanya,” in ji majiyar.
An ce su mutum biyun abokai ne masu aiki a masana’anta daya, kuma duk kokarin da aka yi don shika tsakani a lokacin fadan hakan ya ci tura.
Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, SP Benjamin Hundenyin, ya tabbatar da aukuwar lamarin.
Ya ce suna ci gaba da bincike domin kamo wanda ya yi kisan ya arce don ya fuskanci hukunci