Hira da Saurayin da ya kashe budurwarsa Da Sihiri Saboda Ta Auri Wani.
Duk Musulmi da ya ji wannan hirar da ankayi da wannan yaro yake fadin kalamai tabbas kasan babu sha’anin sanin Allah a rayuwarsa.
Wanda irin wannan kalamai nidai bazan iya rubuta irin wadannan kalamai da yayi amfani da shi sai dau ku saurara kuji yadda abun yake.
A wani labarin kuma wani mutum dan shekara 42 mai suna Ibrahim Adamu Mohd ya kashe kansa ta hanyar rataya a unguwar Kanti da ke karamar hukumar Kazaure a jihar Jigawa bayan budurwarsa ta auri wani mutum.
An tattaro cewa mazauna garin Kanti sun wayi gari a safiyar Lahadi, 12 ga watan Yuni, inda suka tarar da mutumin da igiya a wuyansa, ya rataye a jikin bishiya.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Jigawa, DSP Lawan Shiisu Adam, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Litinin, ya ce marigayin dan asalin kauyen Gayawa ne da ke karamar Hukumar Ungogo ta Jihar Kano.
Ya ce Ibrahim ya kashe kansa ne ta hanyar rataya a kan titin Daura Road hannun riga da Baushe a garin Kazaure a wani gini da ba a kammala ba.
Kakakin na Hukumar Yansanda ya ce an samu katin gayyatar aure da katin SIM guda biyu a hannun mamacin.