• Sun. Nov 10th, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Yadda Wani Matashi Ya Kashe Mahaifinsa Saboda Ya Bata Masa Rai

ByLucky Murakami

Oct 30, 2022

Rundunar ‘yansandan jihar Legas ta kama wani mutum mai shekara 21 da ake zarginsa da laifin kashe mahaifinsa mai kimanin shekara 70.

Mai magana da yawun rundunar ‘yansandan jihar SP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da faruwar wannan lamari.

Hundeyin ya ce, lokacin da ‘yansanda da ke Abule suka samu rahoton kisan daga matar wanda aka kashe, wadda kuma ita ce mahaifiyar wanda ya yi kisan.

Rahoton ya nuna cewa, da yammacin ranar Asabar, wanda ake zargin ya yi amfani da wuka mai kaifi wajen kashe mahaifin nasa a dakinsa,“Wanda ya kawo korafin ya bayyana cewa an tafi kai mahaifinsa asibiti da ke Oke-Odo, wanda kuma a nan ne suka tabbatar da mutuwarsa.‘Yansanda sun je wajen da wannan abin ya faru inda suka dauki gawar zuwa babban asibitin Isolo wadda aka ajiyeta a wajen ajiye gawawwaki.

“An kai wanda ake zargin sashen masu kisan kai da ke ofishin ‘yansanda masu binciken kwakwaf domin ci gaba da bincikensa,” in ji shi.

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *