• Sat. Oct 12th, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Yadda Wani Matashi Ya Rataye Kansa Bayan An Sace Masa A Daidaita Sahu

ByLucky Murakami

Oct 21, 2022

Wani matashi mai shekaru 25 a Jos, babban birnin Jihar Filato, ya kashe kansa sakamakon sace masa Keke Napep guda biyu mallakin ubangidansa da wasu batagari suka yi.

Rundunar ’yan sandan jihar ta ce bayan tsintso gawar matashin a dakinsa, tana zargin ya rataye kansa ne a ranar da wani ya ritsa shi da bindiga ya kwace masa babur na biyu.

Wani dan uwansa na jini mai suna Mista Adukuchili Angai ya bayyana wa Aminiya cewa matashin ya dauki ransa ne sakamakon damuwar da ya shiga.

“A farkon shekarar nan ne margayin ya samu hayar babur mai uku a hannun wata mata don ya rika aika mata kudi kowanne mako, abin bakin ciki, sai ya ara wa abokinsa amma aka sace.

“Matar ta kai shi kara gurin ’yan sanda aka kama shi, sai da ya yi sama da mako guda a hannunsu, sannan aka sake shi tare da neman ya biya kudin babur din da kadan-kadan.

“Ya fara biya makonni kadan sai kuma ya kasa ci gaba, sai ya tunkari wani mutum mai babur din da zummar yin aiki ya aika masa kudin a kullum, don ya samu biyan wancan babur din da aka sace.

“Sai dai a ranar 13 ga watan Oktoba lokacin da yake dawowa gida daga aiki sai wani mutum dauke da makami ya kwace babur din.

“Ya dawo gida cikin bacin rai ya hadu da wasu abokansa inda ya bayyana musu abin da ya faru kuma ya yi barazanar kashe kansa.

“Ba wanda ya dauke maganar da muhimmanci, har sai da innarsa ta dawo gida daga gun sana’arta ba ta gan shi ba,bayan ya saba dawowa gida kafin karfe 7 na dare saboda dokar hana babur mai uku bayan karfe 6:30 na yamma.

“Sai da ta gaji ta leka dakinsa sannan ta hango shi a rataye da wata igiya ba rai.

“Ihun da ta yi ya ja hankalin makwabta, bayan ta kira mu a waya, nan take muka kai rahoton lamarin ga ‘yan sanda a Nasarawa Gwom, in ji Angai.

Ya kuma ce a na zargin wani mai gyaran babura da sace baburin kasancewar an sha kama shi yana dauke-dauke a unguwa, inda aka tisa keyarsa har zuwa gidansa da ke unguwar Angwan Rukuba kuma aka gano babura guda 10 a boye.

Angai ya ce daga nan ne suka mika shi ofishin `yan sanda na Nasarawa Gwom, sai dai daga baya fusatattun matasa unguwar sun afka wa ofishin, inda suka kone shi kurmus.

A nasa bangaren, kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Filato, DSP Alabo Alfred da ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce tuni sun kaddamar da bincike.

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *