Taka wa wani saurayi birki kan zuwa zance wajen budurwarsa, har sai ya tura wakilinsa domin neman izinin iyayenta, ya dagula wa matashin lissafi.
Wani matashi da ya shafawa fuskarsa toka, wajen yi wa wadannan sharuda tawaye, ya gamu da fushin al’umma.
Matashin mai suna Munkaila Suleman, da ke garin Rukku ta karamar hukumar Kura, ya gamu da gamonsa.
Lokacin da yake zance da budurwarsa tasa, mai suna Humaira Idris, bayan dawowar mahaifinta, zai shiga gida da daddare.
Sai ya ganta suna tadi, nan take ya korata gida. Bayan ya korata gida, sai ya koma kan saurayin nata mai suna, Munkaila, wanda kuma ya ce masa, “tuni na ce, in da gaske ka ke yi ka turo iyayenka Ka ki”.
Sannan kuma ya gargade shi, kan ya dai na zuwa wajenta amma ya ki.
A nan ne ganin mahaifinta ya kori yarinyar, ya kuma nuna fushinsa. Hakan ta sa ya dunkuke hannunsa ya kai wa mahaifin bugu ya ci gaba da naushinsa a ciki, inda yayi sanadiyar kai ta asibiti kuma likita suka yi mata dinki inda ya ji mata rauni.
Bayan masoyin mai suna Munkaila ya fada hannun jami’an tsaro sai idonsa ya raina fata.
Bayan kammala bincike an gurfanar da shi gaban kotun Shari’ar Musuluncin ta Kura,
Mai shari’a Malam Ibrahim Isa Usman. Insifekta Nasiru Dan sakkwato ya karanta masa tuhumar da ake yi masa, Nan take ya amsa laifinsa. Inda Mai shari’a Ibrahim Isa ya ce, wanda ake tuhuma ya amsa laifinsa. Yanzu haka kotun bias jagorncin Mai sharia Malam Ibrahim Isa Usman ta daga kara zuwa ranar 17/10/2022.