Cikin wani bidiyo da yake yawo a kafafen sada zumunta anga wata mace me kamar maza tana daukar buhun masara wanda hakan ya bawa alumma mamaki matuka ganin yadda akasan mata musamman na hausawa basu saba da irin wadannan ayyuka na karfi ba.
Amma kuma wannan bidiyo da amihad.com ta samo wasu da yawa suna tambayar tayi wannan abu ne dan a dauki bidiyonta wasu kuma suna cewa neman halak dinta takeyi da wannan sana’a ta dako.
Amma kuma cikin bidiyon abinda amihad.com ta gano shine akwai bokitin tallar wannan budurwa a gefe tare dana abokiyar tallan nata.
Bugu da kari kuma anji muryar wani daga cikin mazan yana cewa taci kudi, ma’ana an asaka mata gasa ne idan tayi za’a bata wani kudi.
Koma dai menene wannan abu hakika ya dauki hankulan mutane matuka musamman a shafin TikTok.
Ga bidiyon nan ku lalla a kasa domin ganewa idonku:
Gaskiya wannan babban abin mamaki ganin yadda wannan budurwa take daukar buhun masara musamman duba ga al’adar hausawa bata bawa mata irin dama ba. Da yawa daga cikin matan hausawa sun saba da aikace aikace na gida yayinda su kuma maza suke fita don nema.
Likitoci Sun Manta Almakashi 2 Acikin Wata Mata Har Shekara 20
Tun bayan yi mata aiki a wani asubiti wanda ba a baiyana sunan sa ba ,ta ringa jin mintsini a cikin ta sosai wanda ya jawo komawar su asubity don duba mai ya faru bayan an yi mata aiki a cikin ta.
Tun da farko dai matar na fama da ciwon ciki, bayan kwakkwaran bincike da likitoci suka yi sun gano matsalar ta babbace wanda dole a yi mata aiki a cikin na ta.
Bayan an kara yin bincike ,an gano cewa a kwai wani karfe a cikin inda likitoci suka ce dole a yi mata aiki don ciro abun da ke cikin cikin ta.
An gano cewa likitocin da su kayi taba yi mata aikin tunda farko ne suka manta “Alkamashi har guda biyu a cikin matar.
A binciken da kayi angano cewa alkamashin sun kai tsahon shekaru 20 a cikin na ta.
Wannan ya jawo cece kuce matuka a gurin likitohci da ma sauran mutane. Wannan na daya daga cikin abu mafi mamaki da ya faru a cikin asubity.wanda likitoci da dama suka yi tsokaci a maganar.