• Mon. Jun 17th, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Yadda Wata Mata Ta Haifi ‘Ya’Ya 9 A Lokaci Daya

ByLucky Murakami

Sep 12, 2022

Munci karo da wani labari me cike da al’ajabi wanda wata mata ta haifi yara tara a lokaci daya wanda hakan ya bawa mutane mamaki matuka.

 

Kamar yadda majiyar amihad.com ta rawaito wata mata mai shekara 25 da mijinta ‘yan kasar Mali sun haifi ‘ya’ya tara, a wani asibitin kasar Maroko, lamarin da ya karya tarihin Kundin Tarihi na Duniya na yawan ‘ya’yan da aka taba haifa a lokacin haihuwa kuma har yanzu suna rayuwa.

Matar da ta haihu mai suna Halima Cissé, ‘yar shekara 25, ta sa likitoci biyu sun duba ta a lokacin da take da juna biyu don tabbatar da ko tana dauke da ‘ya’ya lamarin da ya bar su cikin mamaki. Jaridar Leadership ce ta rawaito wannan rahoto.

Bayan tabbatar da adadin yawan ‘ya’yan, gwamnatin Mali ta kai ta ita da mijinta zuwa Maroko don likitoci su kula da ita yadda ya kamata.

A 2021 Halima ta haifi yaranta guda tara reras, maza biyar mata hudu, kuma kowannensu yana cikin koshin lafiya, sannan ita kanta tana cikin matukar farin ciki da wannan babbar kyauta da ta samu.

A cikin wata hira da mijinta ya yi da BBC, y ace jariran baki daya suna cikin koshin lafiya.

Matar daga Afirka ta Yamma ta doke tarihin da wata mata ta taba kafawa na haihuwar yara takwas ragas, wanda dukkansu na raye.

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *