Wani labari da yake shigowa amihad.com daga jihar AkwaIbom ƴan sanda sun damke wata mata da ta haɗa baki da wasu ƴan iskan gari suka yi garkuwa da mijin ta mai suna Emmanuel Usenekong.
Kamar yadda jaridar Premium Times ta rawaito Kwamishinan ƴan sandan jihar Olatoye Durosinmi ya bayyana cewa an tuni har an cafke ɗaya daga cikin waɗanda suka yi garkuwa da wannan magidanci kuma har ya fallasa komai
” Bayan sun zo har gida sun yi garkuwa da Usenekong sai suka kai shi can wani wuri suka ajiye shi. Daga nan sai suka fara neman ƴan uwan sa su biya kuɗin fansa.
” Da farko sun nemi a biya su naira miliyan 10 ne kafin du sake shi, amma hakan bai yiwu ba. Daga karshe dai sai suka amince da naira miliyan 2.
” Bayan an kawo musu kudin ne suna rabo, sai wannan magidanci ya sulale daga inda yake ajiye ya arce cikin daji har wasu suka tsince su suka haɗa shi da ƴan sanda masu sintiri.
” Daga nan sai ƴan sandan suka bi sawun waɗannan mutane suka iske su suna ta rabon kuɗi. Ganin ƴan sanda sun diro sai suka arce amma kuma Allah ya basu sa’an cafke ɗaya daga cikin su.
” Shi wannan da aka kama cikin waɗanda suka sace mutumin ne ya fallsa komai, ya ce matar mutumin ne ta kitsa komai, yadda za su sace maigidanta da kuma kuɗin da za su caji ƴan uwan sa su biya.
Ƴan sanda sun ce matar magidanci ta amsa laifi cewa ita ce ta kitsa sace mijin ta, kuma ta yi haka ne saboda baya bata kuɗin kashe masu kauri.