• Sun. Sep 8th, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Yadda Ya Kashe Makwabcinsa Saboda Gudun Biyan Bashi

ByLucky Murakami

Aug 10, 2022

Kamar yadda shafin amihad.com ya sabo kawo muku labarai masu daukar hankali da ban mamaki to a wannan karon ma mun kawo muku labarin yadda wani marar imani ya kashe makwancinsa kawai saboda gudun biyansa bashin da yake binsa.

Mun samo wannan labarri daga shafin Aminiya inda labarin yake cewa:

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Oyo ta damke wani mutum kan zargin kashe makwabcinsa da ke bin sa bashi.

Mai magana da yawun rundunar, Adewale Osifeso, ya ce wanda ake zargin ya yi ikirarin ya kashe makwabcin nasa ne don kubuta daga bashin da yake bin sa.

Ya ce bayan kashe marigayin, wanda ake zargin ya dauki motar da ya bayar a matsayin jingina na bashin da ya karba ya tsere da ita.

Da yake bayani sa’ilin da suke gabatar da wanda ake zargin ga manema labarai a ranar Talata, Osifeso ya ce wani mai suna Adesope Adeolu ne ya kai rahoto ofishin ’yan sanda da ke Eleyele bayan faruwar lamarin cewa ya ga kofar makwabcinsa a bude, wanda bai saba aukuwa ba.

“Ko da ya bincika, sai ya tarar da makwabcinsa Olusegun Rufus, kwance cikin jini a mace, inda ya yi zargin mai yiwuwa kashe shi aka yi,” inji jami’in.

Ya ce bayan bincike da bayanan sirri da aka tattara, aka kama wanda ake zargin wanda ya tabbatar shi ne ya kashe Rufus don ya kubuta daga bashin da yake bin sa.

“Haka nan, an gano motar da ya jinginar don karbar bashin wadda ya yi amfani da ita ya tsere,” in ji shi.

 

A Wani Labarin Kuma Ambaliyar Ruwa Ta Kashe Mutane 3, Ta Rushe Gidaje 495 A Kano

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta jihar Kano (SEMA), ta ce ambaliyar ruwa ta kashe mutane uku tare da raba iyalai 495 da muhallansu a Karamar Hukumar Ajingi da ke jihar.

Babban Sakataren hukumar, dakta Saleh Jili ne, ya bayyana hakan a ranar Litinin a Ajingi, yayin da yake raba kayan agaji ga wadanda abin ya shafa, ciki har da iyalan mutane uku da suka rasu.

Jili ya lissafa yankunan da lamarin ya shafa da su hada da Toranke, Kara Malama, Chuna da Balare.

Ya ce lamarin da ya faru bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya a ranakun 3 da 4 ga watan Agusta, ya shafi mutane 495 da lamarin ya rutsa da su, ya kuma kashe uku da jikkata mutum daya.

“A madadin Gwamna Abdullahi Ganduje, mun zo nan ne domin jajanta wa wadanda abin ya shafa tare da raba musu wasu kayayyaki.

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *