• Sun. Sep 8th, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Yadda Ya Shigo Daki Ya Kama Matarsa Da Kwarto

ByLucky Murakami

Aug 17, 2022

Duniya ina zaki damu, wani magidanci ya tona asirin yadda ya shigo otel bazata ya taras da matarsa tana cin amanarsa da kwarto a dakin otel inda wanda ya shaida cewa dama halinta ne.

A wannan lokaci irin wadannan abubuwa nada hau-hawa wajen faruwa tsakanin maza da mata wanda ya akamata a nemi mafita.

Kamar yadda amihad.com ta binciko, bugun zuciya ya kama wani mutum, Udemeh Ukarette, mai shekaru 34, a yayin da ya kama matar sa, Joy Ukarett da wani kwastoman ta wani otel.

Shekarun Udemeh da Joy 16 da aure amma ba su samu haihuwa ba, inda ta ce tayi hakan saboda ta samu ciki tunda shi mijin na ta ya kasa.

Jaridar PM EXPRESS ta ruwaito cewa, wannan abu ya faru ne a layin Toyin Giwa na yankin Afonka Shasha da ke jihar Legas.

Jaridar ta ce, Joy ta sanar da mijinta kuma ya aminta kafin ta kwanta da wannan kwastoman na ta, inda abin ya juya ta fara jin dadin tarayyar su shine ta cigaba.

Da Udeme ya ce ta yanke alakar ta da wannan mutumin shine ta bayyana mijin ba za ta daina ba kuma ta ce mutumin shine babban kwastoman ta sannan ta yi ikirarin idan ya matsa ma ta za ta raba auren su ta komawa daduron ta.

Udemeh da Joy wanda ‘yan asalin garin Anan ne na jihar Akwa Ibom sun bayyana cewa, sun nemi magani na asibiti da na gargajiya amma har yanzu ba wani labari.

Udemeh ya kai karar matar sa kungiyar su ta ‘yan Akwa Ibom a cibiyarsu ta jihar Legas, inda aka yi kokarin a sulhunta amma Joy ta yi mursisi akan ba za ta yanke alaka da sabon saurayinta

Sai dai ta amince za ta cigaba da zama a matsayin matar Udemeh kuma tana tarayya da saurayin na ta.

Kadan Daga Cikin Abubuwan Dake Hana Mata Shiga Aljannah Koda Kuwa Suna Sallah

1) Duk Matar da take da aure tayi zina.

2) Duk Matar da ta Mallaki Mijinta ta hanyar asiri ko ta hanyar tsafi

3) Duk Matar data Hana kishiyarta ta zauna da Mijinta lafiya

4) Duk matar da ta raba mijinta da ‘ya’yansa,ko ta Hanyar Asiri ko Yaudara

5) Duk matar data raba mijinta da Yan uwansa ta hanyar asiri ko yaudara

6) Duk matar da tayi asiri akan saukarwa kishiyarta jinin haila duk ranar kwananta sai haila tazo mata

7) Duk matar da tasa aka daure mahaifar kishiyarta,don kar ta haihu

8) Duk matar data dauko ciki a waje ta bawa mijinta,kuma ta tabbata ba nasa bane

9) Duk matar da tayi daurin baka ga mijinta don yayi mata kishiya.Ma’anar baka shine: Duk ranar da zai kwana a dakin kishiyarta sai ya zamanto bana miji ba.Amma idan ya dawo dakin matsafiyar sai ya dawo namiji

10) Duk matar data nemi mijinta ya saketa,alhali baya cutar da ita.Kuma ba yadda ya iya

11) Duk matar da bata godewa mijinta bisa ga irin abubuwan da yake mata na Alkhairi

12) Duk matar da take cutar da mijinta da bakinta

13) Duk matar da batayin wankan janaba, bayan ta sadu da mijinta,ko batayin wankan haila ko biki

14) Duk matar da take tona asirin mijinta a cikin kawayenta

15) Duk matar da take annamimanci

16) Duk matar da take sa kayan da yake nuna tsiraicinta,irin wanda musulunci yake fada akan irin shigar yahudawa da nasara

17) Duk matar data kara gashi akan nata

18) Duk matar da tilastawa mijinta yayi mata wani abu wanda ba zai iya yi ba

19) Duk matar data dauki dan wani ta bashi Mama (Nono) bada izinin Mijinta ba

20) Duk matar da zata cewa Mijinta tunda muke dakai meka taba yi mini.

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

One thought on “Yadda Ya Shigo Daki Ya Kama Matarsa Da Kwarto”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *