• Thu. Mar 28th, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Yadda Yajin Aikin ASUU Yasa Wani Ɗalibin Rungumar Sana’ar Dafa Indomie Da Kwai

ByLucky Murakami

Sep 11, 2022

Bayan shafe sama da watanni shida ana fafata yajin aiki, wani dalibi ya zabi abinda yafi dace masa kamar yadda majiyar amihad.com ta tabbatar.

Jaridar Premium Times ta rawaito cewa wani dalibin Jami’ar Usmanu Danfodiyo UDUS dake jihar Sokoto Usman Abubakar-Rimi ya fara sana’ar siyar da indomie da kwai a dalilin yajin aikin ASUU da yaki ci yaki cinyewa a kasar nan.

Abubakar-Rimi wanda ke shekarar sa ta karshe a karatun likitanci da ya ke yi ya ce zaman gida da ya ishe shi ya sa ya fara sana’ar saida da abinci.

” A dalilin wannan sana’a da nake yi yanzu na tara kuɗi sosai. Baya ga indomi da kwai da nake yi a shagon ina kuma siyar da masa, farfesu, shinkafa da wake da tsire sannan kuma akwai POS da na buɗe duk a cikin shagon.

“Farantin abinci kowace iri a shago na naira 200 ne amma farashin na iya karuwa bisa ga abinda mutum ke so a kara masa a cikin abincin.

Abubakar-Rimi ya ce baya ga wannan shago da ya bude a cikin garin Sokoto yana kuma da wani shagon da yake siyar da kayan sawa na maza da mata a titin Fodio.

A karshe ya yi kira ga sauran ɗalibai su rungumi sana’a maimakon zaman gida da suke yi.

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *