Kamar yadda kuka sani hukumar NBC ta haramta jin wakar Ado Gwanja yadda ta fitar a wata sanarwa wadda muka kawo muku a baya.
Sanarwar da tace an dakatar da sanya wakar ne a radiyo da talabijin sabo da wasu kalamai da ya ke yi a cikin baitocin waƙar, waɗanda su ka saɓa da dokokin hukumar da kuma al’adar Hausawa.
Sanarwar tace waɗannan baitoci da suke cikin wakar ta Warr sun saɓawa sashe na 3, 18, 2(c) na hukumar dake kula da kafafen yada labarai ta kasa NBC.
Saɓawa wannan umarni na hukumar NBC ga kafafen yaɗa labarai na rediyo da talabijin zai iya sanyawa a hukunta kafar yaɗa labaran, inji sanarwar.
Sai dai kuma yan mata wanda suka hada da Jaruman kannywood sunci gaba da tiqar rawar wannan waka a shafukan su na sada zumunta wanda abun ya zaman kamar gasa.
A gefe guda kuma, amihad.com take samu a yau shine an maka shahararrun mawaƙan zamani na Arewa da fitattun jaruman TikTok a gaban Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke yankin Bichi a Kano bisa zargin rashin tarbiyya.
Duk da cewa majiryarmu ba ta samu kwafin ƙarar ba, amma majiyoyi sun ce laifuffukan sun haɗa da wakokin rashin tarbiyya da rawar TikTok da ke da alaƙa da lalata tarbiyyar al’umma.
Sai dai majiyar tamu ta samu kwafin wasikar da kotun shari’ar Musulunci ta rubuta wa ƴan sanda na neman a binciki koke-koken da ke gaban masu gabatar da ƙara.