Abun tausayi Alaramma Musa Mai Dori, sanannen malamin makarantar Isilamiya ne a Unguwar Dabai, wanda wasu ‘yan kungiyar sa-kai da ke Unguwar Kankare makwabciyar Unguwar Dabai a karamar Hukumar Gwale a Jihar Kano suka yi wa wannan mutum kisan gilla.
Amihad.com ta samu rahoton cewa dukan da ‘yan kungiyar sa-kai suka yi wa Malam Musa Mai Dori a ofiahinsu ranar Lahadin da ta gabata bayan da wata ta zarge shi da laifin satar wani jariri sabuwar haihuwa, wanda yake kokarin cetowa daga cikin bola da aka jefar da shi ya yi sanadiyyar mutuwarsa.
Mai Dori ya kasasance yana da shekara 50 da haihuwa, sannan yana da matan guda biyu, Khadija da Sha’awa da ‘ya’ya 16.
Dan uwan mamacin, Muhammad Ashiru Salisu, wanda ya yi magana da manema labarai ya ce, abin da ya faru wani abu ne na rashin imani wanda kuma aka shirya shi, domin yaran da suka aikata wannan aika-aika sun san malamin kwarai da gaske.
Salisu ya ci gaba da cewa, alaramman yana da kyakkyawar mu’amala ga dukkan mutanen da ke hankin.
Ya ce, “Da yamma muka samu labarin kisan gillar da wasu ‘yan kungiyar sa-kai na unguwar Kankare suka yi wa wannan mutum.
“Lamarin ya faru da safe ne, mu kuma mun samu labarin da yamma, malam ya bar gidansa a wannan safiya, yayin wucewa ta hanyasa, sai ya ga wani jariri sabun haihuwa a cikin wani ramin bola, a kokarin ceton jaririn ne, wata mata da ke bayansa ta kama ihun cewa wai malamin yana son satar jaririn ne.
“Babu shakka al’ummar Unguwar Dabai sun yi alkawarin bin wannan lamarin har karshensa domin tabbatar da gaskiya ta yi halinta.
“Matasan yankin sun yi kokarin daukar fansa kan abin da ya faru, kasancewar malamin ya koyar da mafi yawancinsu, bayan haka kuma shi ne ke taimaka wa jama’a idan matsalar ta kunno kai. Suka ce suna zargin wannan wani shiryeyyen al’amari ne.”
A nasa bangaren, babban dan mamacin, Abdussalam Musa cewa ya yi, “An daki mahaifina har takai ga mutuwasa, rahoton likitoci ne ya nuna an yi ta dukansa a kirjinsa har sai da zuciyarsa ta fara kwararar da jini. Ba za mu bar wannan lamari ya mutu kamar yadda malam ya mutu ba. Za mu bi lamarin har zuwa karshensa,” in ji shi.
Rahotanni sun nuna cewa mutane bakwai da ake zargi da aikata wannan mummunar lamari an kama su suna hannun ‘yan sanda a Rijiyar Zaki da ke Jihar Kano.
Da aka tuntubi kwamandan kungiyar sa-kai na Jihar Kano, Shehu Rabi’u ya ce ofishinsa bai samu wannan labari ba, amma ya yi alkawarin bincikewa zai kuma sanar da manema labarai halin da ake ciki.
A nasa bangaren, kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce mutane shida da ake zargin aikata wannan laifi suna hannu.