• Sat. Jun 22nd, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Yadda Za Ki Fahimci Soyayyar Gaskiya Daga Namiji

ByLucky Murakami

Aug 16, 2022
Yadda ake gane soyayyar gaskiya

Barka da zuwa sau da yawa mata kan kasa fahimtar ko namiji yana son su ko kuma shakuwa ce da abotaka tsakanin su da shi.

Ga kadan daga cikin wadan su alamomin da za su tabbatar maki lallai namiji na son ki, kuma so na gaskiya da soyayya.

1. Tausayi:

Wani irin ji ne da ke ratsa zuciyar duk wani namiji da ya kamu da ciwon son mace. Tausayi yana daya daga matakan farko da ke tabbatar wa mace lallai namiji yana gab da, ko kuma ya kamu da son ki.

Za ki ga abu kadan wanda bai taka kara ya karya ba, namiji yana tausayawa mace, ciwo kadan za ki ga yana nuna matukar kulawarsa da tausayin sa gare ki. Yar’uwa ki kula duk namijin da ke jin tausayin ki, to yana maki so na gaskiya amma duk da namijin da baya tausayin ki to da wuya yayi miki so na gaskiya.

2. Sadarwa:

Idan namiji yana matukar sonki, za ki rika samun kiran wayarsa ako da yaushe, baya iya zama na tsawon lokaci ba tare da ya kira ya ji lafiyarki ba.

So ke saka ki zama ta farkon wacce zai yi magana da ke, bayan tashin sa daga bacci, haka kuma ke ce ta karshe da zai yi sallama da ita kafin ya kwanta.

Za ki rika samun sakon sa na wayar sadarwa (SMS). Haka kuma idan kika yi kira shi duk abin da yake yi zai ajiye, ya dauki kiran wayarki, ko ya dawo maki da sakon da kika tura masa.

Yar’uwa ki kula namijin da baya damu da ya kira ki ba, sai in ke kin gaji dan kanki kin kira shi, ko in kin tura masa sako, to kada ki bata lokacin ki a gare shi, domin zai yi wuya ya so ki.

3. Kasancewa Da Ke:

Namiji kan so kasancewa tare da wacce yake so a koda yaushe, baya gajiya da ganinta, koda baya da lokaci zai saman wani dan kara min lokaci domin kasancewa tare da ita.

Duk namijin da baya kiran ki, sai dai ke dan kanki ki nemi ku hado, to shima yar’uwa ina maki tsoron anya wannan namijin da gaske yana sonki kuwa?. Saboda wanda ke sonki na gaskiya, yana son kasancewa da ke a koda yaushe.

4. Satar Kallun Ki:

Duk namijin da ya kamu da sonki, baya gajiya da kallun ki. Idan kuna tare ki kula, abu kadan za ki yi, zai ya tsora maki ido, wani lokaci ma za ki kama sa yana satar kallun ki.

Haka kuma zai rika kokari ya tausasa idon sa wurin magana da ke, in kika kula za ki iya hango tausayi dakuma soyayya a idonsa.

5. Gabatar Da Ke Ga ‘Yan’uwansa:

Duk namijin da ke kaunar ki saboda Allah, zai yi kokarin gabatar da ke ga ‘yan’uwansa da abokaninsa. Baya jin kunya ko wani haufin nuna ki a matsayin wacce yake so, yake kuma fatan ki zama uwar ‘ya’yansa.

Yar’uwata ki kula, duk namijin da kike zaune da shi, yana maki boye miki asalin sa ko iyayen sa ko kuma abokaninsa, to wannan namiji yana da wata manufa daban a gare ki.

Yar’uwa ki yi hakuri ki kama gaban ki, ina shaida maki zai bata maki lokaci ne a banza ba soyayyan gaskiya yake miki ba.

6. Yarda Da Aminci:

Namiji na yarda da amincewa ga macen da yake so. Zai rika gaya maki sirinsa, musamman dangane ga abin da ya shafi aikinsa.

Zai gaya maki sirri kansa da yake tsoron gaya wa abokaninsa, saboda ya yarda da ke, baya taba tunanin za ki tuna mishi asirin sa. Idan namiji na maki boye-boyen sirrukan sa, to ki bincike son da yake maki.

7. Kyauta:

Kyauta na daya daga cikin alamomin da za su tabbatar maki cewa namiji na sonki so na gaskiya. Wanda ke sonki baya jin komi a ransa idan ya maki kyauta, koda mutunin nan talaka ne, a koda yaushe fatan sa ya yi abin da zai faranta maki rai, ta hanyar saya maki wani abu ko mai kankantar sa, muddin ya san zai saka ki farin ciki.

Sai dai ba lallai bane a samu ko wane namijin a hakan, saboda ita kyauta wani hali ne wanda bakowa Allah ya bashi ba daga jini ne, wani duk son da yake maki sai ki same sa marowaci, baya iya wa ko kansa alkairi balla ya yi maki.

Yar’uwa sai ki kula in dai kin samu wasu daga cikin alamomin da aka kawo, amma kuma kin same sa da halin rashin maki kyauta, sai ki yi hakuri, rowar a jininsa take.

8. Abokai:

Abokai suna daga cikin alamomin da za ki fahimce cewa namiji yana kaunar ki. Ki kula in abokanansa na gaya miki cewa baya da aiki sai masu hirar ki, abu kadan zai ya ce “wance kaza” to wannan mutum yana sonki kuma so na gaskiya.

9. Tsara Rayuwar Sa Da Ke:

‘Yar’uwa ki lura a duk lokacin da kuna tare da shi, yana kawo zancen auren ku kamar ya ce maki, lokacin auren mu za a yi kaza ko kuma ‘ya’yan mu kaza, yana dai kokari tsara rayuwarsa tare da ke. To wannan mutunen yana maki so na gaskiya,so kuma na aure.

10. Shan Minti:

A duk lokacin da namiji yake nuna zalamarsa a gare ki, kamar son yayi maki kiss, ko ya rungume ki, to wannan ba saurayin kwarai ba ne.

Duk namijin da ke sonki saboda Allah, yake kuma muradin ki zama uwar ‘ya’yan sa, ba zai fito maki da kwadayin sa a fili ba, har yana kokarin ya sa ki sabawa ubangijin ki.

‘Yar‘uwa ki kula da irin dangin wadannan samarin na zamani, saboda su suka fi yawa awannan lokacin. Kina kuskure kika bari ya fara taba ki da sunan wai ya nuna maki yanda yake jinki a ransa ta hanyar rungumar ki ko ya yi maki kiss, to tabbas shaidan zai shiga har ya kai ku afkawa juna daga nan duk son da yake maki zai guje ki, muddin ya samu abin da ya ke so.

In kuma ma Allah ya kaddari kuka yi auren ba wani mutuncin ki zai gani ba zai kuma rika zargin ki. Yana tunanin bada shi kadai kika saba ba. ‘Yar’uwa ki kula in wannan bai taba farowa da ke ba na tabbatar ya faru da kawar ki ko kuma ‘yar’uwar ki, don haka sai ki kula sosai.

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *