• Sun. Sep 8th, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Yadda Za’a Magance Matsalan Warin Baki Cikin Sauki

ByLucky Murakami

Mar 10, 2024
Maganin warin Baki Sadidan

A wannan makon na kawo muku bayanin yadda za ku lura da hakorinku, wato- cire dattin hakori da kuma kara wa hakorinku fari da kuma lafiya.

Ana so ku rika wanke bakinku da man goge baki ko aswaki akalla sau biyu duk rana, hakan zai sanya hakorinku ya yi haske.

Idan kana da dattin hakori sai ka nemi man goge baki kamar daya daga cikin wadannan: Colgate da Rembrandt da 3D Crest da Listerine da Akuafresh da sauransu, sannan kuna goge hakorinku da shi.

Za ku iya amfani da bakar soda (Baking Soda) wajen goge hakorinku sau biyu a mako. Kadan ake so ku rika diba idan za ku yi amfani da sodar.

Sannan bayan haka ana bukatar ku kuskure bakinku sosai bayan kun kammala amfani da sodar. Kada don kuna amfani da wadannan sinadaran sai kuma ku daina goge bakinku kamar yadda ya kamata.

Ku rika amfani da kororon da ake shan jus ko lemon kwalba wajen shan jus ko lemon kwalba, hakan zai kara wa hakorinku fari da haske.

Ya kamata ku rage yawan shan kofi da kuma shayin da ba a hada da madara da sauran kayan hadi ba, domin rashin yin hakan zai kara wa hakorinku datti.

Ku guji shan abu mai tsananin sanyi ko zafi, hakan zai taimaka muku wajen kara hasken hakorinki. Ku guji yawaita shan abu mai siga domin kauce wa rubewar hakori.

Ku rika amfani da tsinken sakace hakori bayan kun ci abinci, musamman idan kun ci nama ko kifi da dai sauransu.

Rashin yin hakan zai sanya sauran abinci ya taru a matse-matsin hakorinki, wanda kuma zai iya janyo wa hakorinki rubewa ko kuma ya yi duhu, ko ya haifar muku da warin baki.

Allah yasa mu Dace.
Zaku iya ajiye tambabyoyinku a kasa.

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *